1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

KASAR IRAKI BAYAN CAFKE SADAM

ZAINAB AM ABUBAKARDecember 15, 2003
https://p.dw.com/p/Bvn7
Duk da cewa a halin da ake ciki yanzu haka tsohon shugaba Sadam Hussein na Iraki na hannu, Commandan Amurkan wanda yayi jawabi ta gidan talabijin daga fadar gwamnati ta white house dake washinton,yace har yanzu da sauran rina akaba dangane da cewa tashe tashen hankulan irakin zai kare.
Tun kafin jawaban na shugaban Amurka a ranar lahadi da yammaci,manazarta da masu lura da alamura dakaje suzo sun bayyana cewa babu halaka tsakanin kamun Sadam da rikice rikicen dake cigaba da gudana a Iraki,domin kamun nasa ma a wani bangaren na iya kasancewa makashin tashin hankalin kasar,domin injisu matsalar bata magoya bayan Sadam ko kuma jammiyarsa ta Baath bace,amma matsalace ta harkokin siyasa na cikin gida tare da kyaman sojojin mamayen dake cigaba da kasancewa a wannan kasa.Wasu kuwa na ganin cewa kasancewar sadam a hannu zai dada ingiza masu neman yancin kasa tare da bukatar a gaggauta gudanar da zabe,daukan makamai domin ganin cewa sun kawo karshen mamayen ta kowace hanya,musamman yan shiahn Irakin.Domin yan Shian wadanda ke kyaman manufofin Amurka a wannan kasa yanzu sun samu dama,tunda an cafke Sadam,yanzu kuwa kokarinsu shine suga cewa sojojin mamayen sun basu daman cigaba da harkokinsu a wannan kasa,iniji Juan Cole wanda ke karantar da harkokin tarihi a jamiaar Michigan.
Bababu shakka Sadam ya kasance mutum na farko da Sojojin mamayen ke nema ruwa a jallo,wadanda bayan kashe yayansa biyu Uday da Qusay a garin Mosul,sujka sanar dacewa zasu cafke mahaifin nasu nan bada jimawa ba.Duk dacewa akwai hasashen cewa watakila Sadam ya shige karkashin kasa a kewayen Tikrit,gwiwan Sojin yayi sanyi bayan sun dauki watanni ba tare da samun labari ko kuma gano inda tsohon shugaban irakin yake ba.
Kamar yadda sanarwar Amurkawan ke nuni dashi an ganoshi a bayan wasu na hannun damansa sun fallasa inda yake boye a wani rani dake karshin wani ginin karkashin kasa a wata gona dake wajen garin Tikrit.Rahotanni sun tabbatar dacewa Sadam bai nuna wani taurin kai alokacin kamun nasa ba.Bugu da kari sai bayan da aka yi gwajin jininsa domin tabbatar dacewa tsohon shugaban na Iraki ne kafin aka yayatawa duniya a ranar lahadi da yammaci.
Duk da hasashe tare da zargi da ake nacewa magoya bayan Sadam ne ke da hakkin hare hare da akeyi a ciki da kewayen Iraki,yanayi da aka tsice shi ciki na rashin wata naurarr sadarwa ta tangaraho ko kuma tauraron dan adam,ya tabbatar dacewa baya da wata kima ko kuma martaba a idanun yan Irakin,abunda ke nuni dacewa bashi da hannu a hare haren da ake kaiwa sojojin mamayen.Kuma tun daga ranar kamun nasa ana cigaba da fuskantar munanan hare hare a Iraki.