1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

kasar Iraki ta yaba wa shugaba Trump

Zulaiha Abubakar
March 6, 2017

Gwamnatin Iraki ta yaba wa Amirka game da cire wa kasar takunkumin shiga Amurka da shugaba Donald Trump ya yi.

https://p.dw.com/p/2YibT
USA PK Donald Trump
Donald TrumpHoto: picture alliance/AP Photo/P. Martinez Monsivais

Mahukuntan kasar Iraki sun yaba tare da bayyana gamsuwarsu game da cire wa kasar takunkumin shiga Amirka da shugaba Donald Trump ya yi, a wata sabuwar kwaskwarima da yayi a kan  batun dakatar da wasu kasashen Musulmi shiga Amirka. Hakan dai ya biyo bayan zanga-zanga da kuma shigar da kara da kungiyoyi daban-daban suka yi kan hukuncin da Donald Trump ya yanke tun farkon darewarsa kujerar shugabancin kasar. kamar yadda ministan harkokin wajen kasar Iraki ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a wannan Litinin. 


Ya kara da cewar janye takunkumin abu ne daya dace in aka yi la'akari da Kyakykyawar alakar da ke tsakanin kasashen biyu musamman a kan yaki da ta'addanci. To sai dai wani jami'in  fadar mulki ta White House ya ce ana sa ran Donald Trump zai rattaba hannu a kan wata sabuwar doka a yau a kan hana wasu kasashen Musulmi shida shiga kasar ta Amirka bayan yunkurinsa na farko daya samu tsaiko daga kotu.