1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Isra’ila ta ce a shirye take da janye kawanyar da take wa gabar tekun kasar Lebanon a cikin sa’o’i 48 masu zuwa

September 8, 2006
https://p.dw.com/p/BukE

Israila tab a da sanar cewar a shirye take ta dakatar da kawanyar da take wa gabar tekun kasar Lebanon cikin awa 48, bayan ta gamsu da alkawarin MDD mai cewar zata tsugunar da sojojin ta na kasa da kasa domin hana sufurin makamai ga dakarun Hizbullah. Kasashen Faransa, Italiya da Girka sun yi alkawarin bada jiragen ruwa ga rundunar wadanda zasu rika santiri a gabar tekun Lebanon har tsawon makonni uku lokacin da rundunar sojin ruwa ta kasar Jamus zata karbi aikin. Daman ana ta kai ruwa rana a nan Jamus akann tsayar da lokaci da kuma irin dokokin da rundunar sojin zata yi aiki dasu. Ranar alhamis ne Israila ta dakatar da matakinta na toshe hanyoyin jiragen sama na Lebanon wanda ta fara lokacinda ta kaiwa kasar hari a watan juli da ya gabata.