1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Sin tayi gwajin harbo tauraron dan adam

January 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuU4

Jamian leken asiri na Amurka sunce a karon farko kasar China ta harbo wani tauraron dan adam,tana mai baiyana nata ikon kann harkokin soji da suka shafi sararin samaniya.kasashen Amurka,Japan da Austarlia suka baiyana damuwarsu kann wannan batu bayanda gwamnatin Amurka ta tabbatar da cewa kasar ta China ta gudanar da wannan gwajin.

Gwamnatin Amurkan tace China tayi anfani da makami mai linzami wajen harbo wani tauraron dan adam dake binciken yanayi a karshen makon daya gabata,wanda hakan ya sanya kasar ta Sin kasa ta uku data taba harbo wata naura daga sararin sama,bayan Amurka da tsohuwar taraiyar Soviet.