1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Singapore

Abba BashirSeptember 19, 2005

Masu sauraron mu asalamu alaikum barkan mu da sake saduwa a cikin wani sabon shirin na Amsoshin takardun ku,shirin dake amsa tambayoyin masu sauraro.

https://p.dw.com/p/BwXO
Singapore
SingaporeHoto: dpa

Tambaya: Fatawar Mu ta wanan makon ta fito daga hannun mai saauraron mu a yau da kulum Maryam Ahmad Gazali dake zaune 6 Cole Sreet garin Jos na jihar Palateue a tarayar Nigeria,mai sauraron ta mu dai na son mu bata tarihin kasar Sigapore.

Amsa: Kasar dai ta Singapore dake kan tsibiri a karni na 14 ta taba zama karkashin mulkin kasar Japan,kafin kuma a karni na 16 kasar portugal ta karbi ragamar mulkin kasar ta Singapore,shekaru dari bayan mulkin kasar Portugal,kasar Holand ma ta yiwa kasar ta Singapore mulkin mallaka.A shekara ta 1819 Sir Thomas Stamford Raffles ya zamanto kantoman birtania a gabashin India,kuma ya kafa wasu huldodi na kasuwanci,tsakaninsa da Sultan Johore a tsibirin na Singapore karkashin yarjejeniyar 2 ga watan Augustan 1824.Kasar Japan ta cigaba da yiwa kasar Singapore mulkin malaka tun 1942 har zuwa karshen yakin duniya na biyu a 1945.bayan yakin duniya na biyu ne a 1945 kasar ta Singapore ta zama mai cin gashin kanta,bayan tsame ta daga tsakanin yakunan Penang da Malacca. Kasar dai ta Singapore ta sami yancinta ne lokacin kasar Malaysia sami yancin kanta a watan satumaban 1963,kuma tun daga wanan lokacin ne kasar ta Singapore ta zamanto daya daga cikin sabin jihohi 14 da aka kirkiro daga cikin kasar Malaysia.

A ranar 7 ga watan Agustan 1965,bisa amincewar gwamnatin kasar Malaysia,kasar Singapore ta zamanto jamhuriya mai cin gashin kanta.Jamhuriyar dai ta Singapore ta ,kunshi wasu kanan tsibirai har 63 dake kudancin kasar.A shekara ta 2002 kasar Singapore nada yawan al’umma miliyan 4,452,732,kuma yawancin alumar kasar na zaune ne a birane.A yanzu haka dai akwai yan kasahen India,China, da Malaysia masu yawan gaske dake zaune a kasar.

Harshen Malaya shine harshen da alumar kasar ke amafani da shi,yayin da a hannu daya kuma ake amfanin da harshen turanci wajen gudanar da harkokin gwamnati.Kasar Singapore nada yanayi mai zafin gaske,kuma ana samun ruwan sama a duk fadin shekara,to sai dai an fi samun zubar ruwan sama mai yawa a watan Nuwamba.Kasar Singapore na bin tafarki irin na Democradiya da majalisar dokoki,kuma da kundin tsarin mulkin kasar ake zartar da dokoki,yayin da Piraminista kuma ya zamanto shine a matsayin shugaban kasa da ’yam majalisar ministoci dake goya masa baya.A ranar biyu ga watan janairun 1997 aka gudanar da zabe,inda jama’iyun adawa suka yi takarar kujeru 36.Jamaiyar Peoples Action Party ce ta lashe kujeru 81 na yan majalisun dokoki da aka yi takara a kann su.Bisa tsarin dokokin kasar Singapore tilas ne dukanin yan kasar su shiga aikin soji,har ma da baki da suka dade suna zaune a kasar.Kasar Singapore na daga cikin kasahen duniya shida da aka baiyana a matsayin kasar dake da karancin jamian gwamnati dake ruf da ciki da dukiyar kasa.Singapore dai yace a wasu kungiyoyi na kasahen duniya da suka har da majalisar dinkin duniya da kuma kungiyar ciniki ta duniya,kungíyar cigaban kasahen Asia da kuma Commonwealth.Jamhriyar Singapore nada karin tattalin arziki,kuma ta bunkasa a fuskar masana’antu aiyukan gona da kuma kamun kifi,inda aka kiyasta cewa tana fitar da kifin data kama da ya kai ton 241,000 ga kaduwanin turia.Kasar singapore nada babar tashar jiragen ruwa da ake amfanin da ita wajen kai kayayyaki zuwa kasahen duniya ta Containa.Singapore nada yawan musulmi dakuma sauran mabiya addinai,yayin da a hannu daya kuma Singapore din keda ofisoshin jakadancin a kasahen duniya da dama.

Muna fata Maryam Ahmad dake zaune a jihar Palateun Nigeria ta gamsu da tarihin da muka bata na kasar Singapore.