1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Switzerland za ta maidowa Najeriya wasu kudade

Salissou BoukariMarch 9, 2016

An cimma yarjejeniya tsakanin Switzerland da Tarayyar Najeriya kan batun maidowa Najeriya wasu kudade da suka kai miliyan 321 na dalar Amirka.

https://p.dw.com/p/1I9ck
Zentralbank von Nigeria
Babban bankin Tarayyar Najeriya

An dai samu rattaba hannu kan wannan yarjejeniya, bayan wata haduwa da aka yi a Abuja, tsakanin wata tawaga ta kasar Switzerland a karkashin jagorancin shugaban diflomasiyyar kasar Didier Burkhalter, da kuma mataimakin shugaban kasar ta Najeriya Yemi Osinbajo.

Takardan da aka ratabawa hannu dai ta tabbatar da tsarin maidowa Najeriya wadannan kudaden da tsofon shugaban kasar marigayi janar Sani Abacha a ajiye a can, ta yadda hakan kuma zai tilastawa Najeriya yin amfani su a fannin ayyukan bunkasa rayuwar al'umma a cewar wata sanarwa da aka wallafa ta shafin Internet na ofishin harkokin wajan kasar ta Switzerland.

Bayan dai rasuwar janar Sani Abacha a shekarar 1998 an zarge shi da karkata akalar wasu kudade da yawansu ya kai dalar Amirka miliyan dubu 2,2 daga babban bankin kasar.