Kasashe 10 da suka fi yawan attajirai a Afirka Kudu da Sahara
A mafi yawan kasashen Afirka Kudu da Sahara ana fama da talauci, amma bisa wani rahoto na cibiyar "New World Wealth" yawan attajirai a kasashen ya karu. Shin daga wasu kasashen Afirka mafi yawan attajiran suka fito?
Afirka ta Kudu
Kasar Afirka da ta fi yawan attajirai ita ce Afirka ta Kudu. Manyan attajirai na miliyoyin dala, su dubu 46 da 800 ke a cikin rukunin attajirai na "High-Net-Worth-Individuals" (HNWIs) suke zaune tsakanin biranen Cape Town da Johannesburg, yawansu kuma na karuwa. A yanzu Jamus na da attajirai kimanin miliyan 1.1 da suka mallaki akalla miliyan na dala.
Najeriya
Bisa bayanan mujallar tattalin arziki ta Amirka- Forbes, dan Najeriya Aliko Dangote ya fi kowa kudi a Afirka. An yi kiyasin dukiyarsa daga masana'antun abinci da siminti da man fetir ta kai dalar Amirka miliyan dubu 18.2. Yana daya daga cikin attajirai dubu 15 da 400 'yan rukunin "HNWIs" a Najeriya. Amma kasar na cikin kasashen Afirka da suka fi yawan 'yan gudun hijira a Turai.
Kenya
Dukiyar attajirai 8500 da suka mallaki miliyoyin dalar Amirka a Kenya ya yi daidai da kashi biyu bisa uku na jimillar dukiyar kasar. Bambamcin ya yi yawa matuka. Yayin da kowane daya na attajiran Kenyan ya mallaki kimanin dalar Amirka miliyan 83, kusan rabin 'yan kasar na rayuwa da abin da bai kai dala biyu a rana ba.
Angola
Arzikin man fetir da Angola ta samu ya janyo karuwar yawan manyan attajirai a kasar tun bayan shiga wannan karni. Yanzu yawansu ya kai 6400 a rukunin HNWIs a kasar, abin da ya ninka har sau shida idan aka kwatanta da shekaru 15 baya. A kasar ce mace mafi arziki a Afirka take, wato Isabel dos Santos 'yar shugaban kasa. Dukiyarta ta kai dalar Amirka miliyan dubu 3.2.
Mauritius
Ko da yake kasar Mauritius da ke zama wani tsibiri a tekun Indiya na da yawan al'umma miliyan 1.3, amma tana da attajiran miliyoyin dala da yawansu ya kai 3200. Harkar yawon bude ido na bunkasa a kasar sannan Mauritius na zama wata kasa da ke da sassaucin haraji.
Namibiya
Da kashi 25 cikin 100 na jimillar tattalin arziki, aikin hakan ma'adanan karkashin kasa shi ne mafi muhimmanci a bangaren masana'antu a Namibiya. Lu'ulu'u ne hajja mafi muhimmanci da kasar ke sayarwa ketare. Ko da yake kasar da taba zama karkashin mulkin mallakar Jamus na da al'umma miliyan biyu, amma akwai 'yan Namibiya 3100 da kowanensu ya mallaki dukiyoyi fiye da dalar Amirka miliyan daya.
Habasha
Habasha ce ke a matsayi na tara a jerin kasashen Afirka 10 na Kudu da Sahara da suka fi yawan attajiran miliyoyin dala. Sun kai 2800 a yanzu. Kwanciyar hankalin siyasa da masu zuba jari daga ketare sun taimaka an samu habakar tattalin arziki a Habasha tun shekarar 2003. Sai dai duk da haka kashi daya bisa uku na 'yan kasar na rayuwa cikin talauci, wato ba sa samun fiye da dala biyu a rana.
Ghana
Zinari da man fetir da 'ya'yan koko su ne muhimman hajjojin da Ghana ke sayarwa ketare. 'Yan Ghana da yawa sun yi arziki saboda wadannan danyun kayayyakin. Mutane 2700 ne attajiran miliyoyin dala a kasar, fiye da ninki hudu idan aka kwatanta da shekaru 15 baya. Baya ga danyun kaya, suna kuma gudanar da harkokin kasuwancin bankuna da gidaje.
Botswana
Attajiran miliyoyin dala 2600 ke zaune a Botswana. A shekarun bayan nan harkar lu'ulu'u ta taimaka an samu attajirai da yawa a kasar. Duk da yawan masu dauke da kwayoyin cutar HIV da yawan marasa aikin yi, Botswana ke a matsayi na hudu na yawan masu samun kudaden shiga a kasashen Afirka Kudu da Sahara.
Côte d'Ivoire
Shekaru takwas da suka wuce aka kawo karshen yakin basasa a Côte d'Ivoire, tun bayan nan kasar ke habaka. Attajiran miliyoyin dala 2300 ke kasar yanzu, yawansu zai karu cikin shekaru masu zuwa. Danyen mai na taka muhimmiyar rawa a nan. Sai dai idan aka kwatanta ci gabanta a duniya baki daya kasar tana baya. Tana a matsayi na 171 daga 187 a tsarin ci gaban al'umma na Human Development Index.