1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe sun ja kunnen Sudan ta Kudu

January 3, 2018

Amirka da Birtaniya da kuma Norway, sun yi kiran martaba yarjejeniyar tsagaita wuta a Sudan ta Kudu wadda aka sanya wa hannu a bara.

https://p.dw.com/p/2qFtR
Südsudan Juba - Riek Machar, Salva Kiir
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Patinkin

Kasashen Amirka da Birtaniya da kuma Norway, sun yi kira ga bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu, da su daina yin kafar ungulu ga yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanya wa hannu a bara a kasar Habasha. Yarjejeniyar dai an tsara ta ne don kawo karshen yakin shekaru hudu da jaririyar kasar ta shiga.

Bangaren gwamnati karkashin jagorancin shugaba Salva Kiir da na 'yan tawaye ne dai ke kai wa juna hare-haren da ya kaiga asarar dubban rayuka a kasar. Kasashen na Amirka da Birtaniya da Norway, su ne dai suka goyi bayan kafa kasar ta Sudan ta Kudu, wadda ta balle daga kasar Sudan a shekarar 2005.

Yanzu dai kasashen sun yi barazanar daukar matakai kan duk wani bangaren da ya saba wa yarjejeniyar baya-bayan nan ta tsagaita wutar.