1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashe sun yi ca kan kisan 'yan Rohingya

September 4, 2017

Kasashen musulmi na yankin Asiya, sun yi suka tare da Allah wadai ga jagorar gwamnatin kasar Myanmar Aung San Suu Kyi dangane da kisan kiyashi da ake yi wa musulmi tsiraru 'yan Rohingya.

https://p.dw.com/p/2jKMX
Rohingya in Myanmar und Bangladesch
Hoto: picture-alliance/dpa/M.Alam

Kasashen musulmi dake yankin Asiya, sun yi suka tare da Allah wadai da jagorar gwamnatin kasar Myanmar Aung San Suu Kyi dangane da kisan kiyashi da ake yi wa musulmi tsiraru 'yan Rohingya. Kimanin 'yan kabilar ta Rohingya dubu 90 dai ne kawo i yanzu suka tsere i zuwa kasar Bagaladesh cikin kwanaki 10 da suka gabata, bayan barkewar rigima tsakaninsu da sojojin kasar ta Myanmar.

Ita ma matashiyar nan wadda ta sami lambar yabo ta Nobel a fannin zaman lafiya, 'yar asalin kasar Pakistan Malala Yusafzai, ta yi tir da shirun da Aung San Suu Kyi ke yi dangane da halin da mutanen ke ciki. Shekaru da dama ne dai ake zaman tankiya tsakanin musulmin, da mabiya addinin Buddha, inda su 'yan tsirarun musulman ke fama da wariya.