1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya na ci gaba da kai caffa ga sabon shugaban Nigeria

May 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuM3

Duk da zarge zargen tafka magudi da akace ya faru, a zaben shugaban kasar da aka gudanar a Nigeria, kasashe daban daban na duniya na ci gaba da kai caffa ga shugaba mai jiran gado , wato Alh Umaru Musa yar´adua.

Sakon fatan alheri na baya bayan nan dai ya fito daga kasashe irin su Brazil da Iran da Cuba da Koriya ta arewa da kuma kuwait.

Idan an iya tunawa a farko farkon makon nan ne, kasashe irin su Italiya da Amurka da Russia da Canada da Japan da kuma kasar Sin,

suka mika na su sakon taya murnar ga shugaban mai jiran gado.

Alh Umaru Musa yar´adua, a cewar hukumar zaben kasar ya samu kaiwa ga wannan nasarar ne, bayan ya doke abokanan karawar sa 24.

To sai dai da yawa daga cikin kungiyoyi masu zaman kansu a kasar da kuma jami´ai masu sa ido na kasashen ketare, sun shaidar da cewa zaben bai gudana a sahihiyar turba ta mulkin dimokradiyya ba.

A dai ranar 29 ga watan nan ne ake sa ran Alh Umaru Musa Yar´adua, zai karbi madafun ikon kasar daga hannun cif Olesegun Obasanjo, da wa´adin mulkin sa ke karewa, bayan tsawon shekaru takwas yana jagorancin kasar.