1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya na ci gaba da nazarin amsar da Iran ta mikawa Mdd

August 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bulm

Kasar Faransa tace kasashe masu fada aji a duniya zasu yarda da fara tattauna matakan warware rikicin nukiliyar Iran ne kawai, idan kasar ta dakatar da aniyar ta na ci gaba da sarrafa sanadarin Uranium.

Wadan nan kalamai dai sun fito ne daga bakin ministan harkokin wajen kasar, Phillippe Douste-Blazy, jim kadan bayan ganawar sa da takwaran sa na Israela a birnin Paris.

Wannan mataki da kasashen masu fada aji ke shirin dauka suka, yazo ne kwana daya, bayan kasar ta Iran ta mayar da martani a hukumance ga Mdd akan irin tallafin da akace za a bata matukar tayi watsi da aniyar mallakar makamin na Atom.

Ya zuwa yanzu dai bayanai sun shaidar da cewa kasashe masu fada ajin na nan na ci gaba da nazarin wannan amsa da kasar ta Iran ta mikawa Mdd a rubuce.

To sai dai kuma, bayanan bayan fage na nuni da cewa a cikin martanin da kasar ta Iran ta mika babu wata alama data nuna na watsi da wannan aniya tata.

Idan dai za´a iya tunawa a farko farkon wannan makon ne shugaban addini na kasar, wato Ayatollah Khameni ya tabbatar da cewa babu gudu babu ja da baya a game da wannan aniya da kasar ta Iran tasa a gaba.