1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen G7 sun cimma daidaituwa

Kamaludeen SaniMay 27, 2016

Kasashen nan bakwai masu karfin tattalin sun jaddada daukar matakan habaka tattalin arzikin duniya.

https://p.dw.com/p/1Iw8z
Japan G7 Gipfel
Hoto: Reuters/J. Watson

Shugabannin Kungiyar G7 da su kammala taronsu a Japan bayan sun amince da wani daftari da ke kunshe da bayanan da suka cimma matsaya,sun sha alwashin daukar duk matakan da suka wajaba domin kara bunkasa harkokin da suka shafi saye da sayarwa gami da magance matsalolin da ke kawo cikas wajen ci gaban tattalin arzikin duniya.

Kungiyar ta G7 ta sha alwashin shawo kan matsalolin tattalin arzikin duniya

Firiministan Japan Shinzo Abe da ke zama mai masaukin baki a yayin kammala taron ya ce :

Japan G7 Gipfel
Hoto: Reuters

''A matsayina na mai shugabantar wannan taron na sadaukar da daukacin lokacina a kan harkokin ci gaban tattalin arziki,kuma ban fitar da tsammani za mu iya magance matsalolin ba.''

Japan G7-Gipfel Barack Obama und Shinzo Abe in Ise-Shima
Hoto: Reuters/T. Hanai

Barazanar Koriya ta Arewa ga Kasashen duniya

baya ga batun tattalin arzki taron ya kuma duba batun barazanar da Koriya ta Arewa take kawowa a tsakaninta da makwaftan kazalika taron ya yi Allah wadai da kutsen da Rasha ta yi a yankin Crimea na Ukraine da kuma China.Ita ma Christine Lagarde Shugabar hukumar ba da lamuni ta duniya a yayin da take tsokaci kan daftarin cewa take:

''Ina fatan daftarin ya faiyace yadda G7 suka amince a kan murandan da aka tsara,sun amince a wasu bangarorin da suke ganin za su sanya jari gami da wasu manufofi da suke ganin bukatar aiwatar da su.''

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ita ma dai batu ne ta yi na harkokin bunkasa jari:

''Za mu ci gaba da ba da himma a bangarorin kasuwanci kuma za mu yi aiki wajen ganin mun kammala yarjejeniyar c kasa da kasa da zuba jarin hadin gwiwa mai suna TTIP.''