1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen kungiyar ASEAN sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta tarihi

January 13, 2007
https://p.dw.com/p/BuUd

Shugabannin kasashen kudu maso gabashin nahiyar Asiya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya mai muhimmanci ta yaki da ta´addanci. A gun taron su na shekara shekara a tsibirin Cebu na kasar Filipins shugabannin kungiyar hadin kan kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN sun amince da wata doka wadda ta tilasta aiki da yarjejeniya wadda ita ce ta farko tsakanin kasashen yankin baki daya. Yarjejeniyar ta yi kira ga kasashen kungiyar ta ASEAN da su inganta hadin kai don rigakafi tare da binciken hare haren ta´addanci. Kungiyar mai membobi kasashe 10 ta kuma amince ta sanya ranar kafa wani yankin cinikaiya maras shinge a cikin shekara ta 2015.