1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Larabawa da Iran

Zainab A MohammadJune 16, 2005

Ayayinda gobe ne ake kada kuriar zaben shugaban kasa a Iran ,kasashen yankin na tofa albarkacin bakinsu dangane da makomar kasar a siyasance.....

https://p.dw.com/p/BvbK
Hoto: AP

Yanzu haka dai idanun sauran kasashen larabawa ya koma kan zaben shugaban kasa a Iran,domin ganin yadda wannan kasa mai mafi yawan alummar darikar shia,zata taka rawa a harkokin Iraki da kuma matsalolinta na Nuclear da kasashen yammaci.

Kasashen larabawa dake makwabtaka da Iran din dai na ganin cewa kowane shugaba zaa zaba a wannan kasa bazai kawo wani sauyin da zaiyi tasiri ba,domin dukka lamuran kasar yana hannun shugaban addini ne wanda kuma ba zababbe bane,dangane da irin tsarin wannan kasa.

Shugabannin kasashen larabawan dai na ganin cewa sakamakon zaben shugaban kasare na gobe bazaiyi wani tasiri ba dangane da matsayin Iran a wannan yanki ,saboda rikicinta na Nuclear da kuma tsamin dangantakarta da Amurka.

Tuni dai jamian Tehran suka bayyana cewa zasu mayar da martani idan Amurka ko Izraela tayi yunkurin afkawa cibiyar sarrafa nuclearnta,ta hanyar amfani da wasu kasashen yankin da suka hadar da Lebanon da yankunan Palasdinwa,ko Afganistan da Iraki ko kuma ta wata hanya daban.

Iraki dai na mai kasancewa babban goro wa Iran a wannan yankin da kuma a dangantaka da Amurka,inji Mustafa alani ,masani kan harkokin tsaro a cibiyar bincike daken yankin gulf dake Dubai.To sai dai ayar tambaya anan itace yaya Iran zatayi amfani da Irakin?

Kasashen dake karkashin mulkin yan darikar sunni da suka hadar da masar da Saudi Arabia da Jordan na tantama kan madafar da iran take dashi kan iraki ,kasar da akaro na farko yan darikar shia sun karbi ragamar mulki,wanda aka danganta da mamaya da Amurka tayi.

Ba tare da laakari da matsayin yan darikar shia a kasar ta iraki ba ,kasashen dake marawa na yammaci baya a yankin ,na na bukatar a sanya yan darikar Sunni cikin harkokin rubuta kundun tsarin mulkin wannan kasa.

Iran wadda wadda keda dangantaka ta kut da kut da a kungiyoyin yan darikar Shia dake Iraki ,wadanda keda mulkin kasar ,bata da wani abunda zata ci moriya daga tsoma baki cikin harkokin kasar musamman dayake akwai dangantaka mai tsami tsakanin ita Iran din da Amurka.

Ana dai cigana da mahawara dangane da yiwuwan samun nasaran dan takara Rafsanjani ,mutuimini da shine kada kadai yace zai inganta dangantakar Iran da kasashen yammaci.

Gwamnatin Iraki dai tayi imani da wannan bayanai na dankara Rafsanjani wanda ya riki karagar mulkin Iran daga shekara ta 1989 zuwa 1997.

Yanzu hakas dai kasashen Larabawa dake wannan yankin ,wadanda kuma tuni suka bayyana tsoronsu dangane da tashe tashen hankula dake cigaba da zubar da jinni a Iraki,zasuyi maraba da dukkan gwamnati da zata inganta dangantaka da Amurka,wanda kuma shine zai kawo karshen barazanar makaman nuclear da iata Iran din ke dashi a wanna yankin na gabas ta tsakiya.

Bandar al-aiban dake shugabantar komitin harkokin waje na majalisar shura dake saudiyya,yace Riyadh taso cigaba da hadin kai da Iran kan harkokin tsaro dakuma taimakawa wajen kawar da makamai na kare dangi daga wannan yanki baki daya.,kuma jamian kasar sun bayyana goyon bayansu.

Ya bayyana cewa Iran na neman goyon bayan kasashen larabawa gabannin kowane irin matsala zata fuskanta da Amurka ko kuma komitin sulhu na mdd dangane da harkokinta na nuclear,to sai dai inji shi babu tabbaci dangane da gabatarwan na Iran.