1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Larabawa na aniyar kawar da bambamci tsakaninsu

Mohammad Nasiru AwalJuly 25, 2016

An bude taron kolin shugabannin kasashen Laraba a kasar Mauritaniya tare da neman hadin kai tsakaninsu.

https://p.dw.com/p/1JVjq
Arabische Liga Mauretanien
Hoto: picture-alliance/dpa/Emirates News Agency

Shugabannin kasashen Larabawa da manyan jami'ai sun hallara a Nouakchott inda suke halartar taron kolin kungiyar kasashen Larabawa ta Arab League. Ana sa rai mahalarta taron za su ba wa tattauna batun samar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa sabon ruhi. Mai masaukin baki kuma shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz shi ne ya bude zaman taron da ke gudana karkashin wani babban tanti a birnn Nouakchott.

Ya ce: "Muna fatan samun sabon yunkurin na duniya kan warware rikice-rikice da suka addabi kasashen Larabawa. Nauyi ne ya rataya a wuyanmu na warare matsaloli tsakanin 'yan uwa, muna da abubuwa da suka hada mu fiye da wadanda za a iya amfani da su don raba kanmu."

A ranar Lahadi ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun nuna goyon baya ga sabon yunkurin kasar Faransa na farfado da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu inda ta shirya wani taron kasa da kasa kafin karshen shekara.