1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen turai na ci gaba da musanta rahoton da EU ta fitar

June 8, 2006
https://p.dw.com/p/Buut

Kasashen turai suna ci gaba da musanta rahoton majalisar mashawrtan turai ta fitar cewa suna da hannu cikin aiyukan fitarwa ko aikewa da wadanda ake zargi da laifin taaddanci zuwa wasu kasashe ko cibioyin tsaro na hukumar leken asiri CIA domin azabtar da su.

Kasa ta bayan nan itace Cyprus,wadda tace,gwamnatin kasar Amurka bata taba sanar da ita ba,dangane da aikewa ko tsare wani wanda ake zargi da taaddanci zuwa kasarta ba,sai dai a 2004 kusan sau 7 ake baiwa wasu jiragen masu zaman kansu na Amurkan sauka a kasar domin wasu matsaloli da suka samu.

Shi dai shugaban majalisar mashawartan turai da ta fidda rahoton,Rene Van Der Lindrn yace wannan rahoto ya kara wayar masu da kai dangane da harkokin hukumar leken asiri ta CIA.