1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen yamma na ci gaba da matsawa Iran Lamba

January 17, 2006
https://p.dw.com/p/BvBu

Kasashen duniya masu fada aji sun cimma yarjejeniyar matsawa Iran lamba akan ta dakatar da binciken data fara a wasu tashohin nukiliyar ta dake cikin kasar.

Wakilan kasashen da suka fito daga Faransa da Amurka da Biritaniya da Russia da Jamus da kuma Kasar sin, sun cimma wannan matsayin ne a lokacin taron kolin da suka gudanar a birnin London a jiya litinin.

A lokacin taron, kasar Amurka ta bayyana cewa bata shakkun watakila sai an yi amfani da karfin sojin wajen hana kasar ta Iran ci gaba da gudanar da aiyuka a tashohin nukiliyar ta ta.

Su kuwa kasashen Faransa da Jamus da Biritaniya, kiran taron hukumar kula da makamashin nukiliya suka yi don tattauna wannan batu, bisa manufar daukar matakin daya dace.

Ana sa ran gudanar da wannan taro na hukumar ta IAEA a ranar biyu ga watan fabarairun wannan shekara da muke ciki.

Kasashen na yamma dai tare da kasar Amurka na zargin kasar ta Iran ne da kokarin kera makamin nukiliya, wanda kuma tuni mahukuntan na Tehran suka karyata hakan da cewa nukuliyar su ta zaman lafiya ce, amma ba ta tashin hankali ba.