1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen yamma na neman hana cinikin fasahohi da Iran

October 24, 2006
https://p.dw.com/p/Buei

Kasashen Amurka Faransa da Burtaniya suna neman komitin sulhu na majalisar dinkin duniya ya haramta sayarda makamai masu linzami da fasahar nukiliya ga kasar Iran tare da kawo karshen yawancin shirye shiryen taimakon fasahohin zamani na hukumar kare yaduwar makaman nukiliya a Iran.

Jamian diplomasiya na majalisar dinkin duniya wadanda suka nemi a boye sunansu sun baiyana cewa,wannan shawarar zata bukaci sauran kasashe membobi na majalisar da su hanawa jamian kasar Iran wadanda suke da hannu a shirinta na nukiliya shiga kasashensu .