1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kashedi a game da makamashin Iran

May 3, 2007
https://p.dw.com/p/BuMI

Britaniya ta yi barazanar cewa idan Iran ta ki dakatar da shirin ta na bunƙasa makamashin Uranium, to zata fuskanci wasu takunkumin na majalisar ɗinkin duniya karo na uku. Wannan dai na daga cikin sakamakon da ya fito a tattaunwar da ta gudana a birnin London wadda ta ƙunshi jamiái daga ƙasashe biyar masu kujerar dundundun a kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya da suka haɗa da Britaniya da China da Faransa da Rasha da Amurka da kuma Jamus. Ministar harkokin wajen Britaniya Magret Beckett ta faɗa a cikin wata sanarwa cewa dukkan ƙasashen shida masu ƙarfin faɗa aji, sun amince a kan hanyoyin da zaá sami cigaba. Ƙasashen sun kuma jaddada goyon bayan su ga jamiín tsare tsaren harkokin wajen ƙungiyar Javier Solana da ya cigaba da tattaunawa da mahukuntan na Tehran. Iran ta nanata aniyar ta na cigaba da shirin nukiliyar.