1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kason kuɗi ga matakan gwamnatocin Nijeriya

August 14, 2010

Gwamnatoci a Nijeriya sun sami kason kuɗi na wata - wata mafi tsoka a tarihin ƙasar

https://p.dw.com/p/OnhM
Hoto: AP

Hukumomi a Nijeriya sun rarraba kuɗin daya kai dalar Amirka miliyan dubu huɗu da 700 ga matakan gwamnatocin ƙasar guda ukku ga watan Yuli. Matakan dai sun haɗar da gwamnatin Tarayya, na jihohi da kuma na ƙananan hukumomi. Kason kuɗin dai shi ne mafi yawa da ƙasar ke rabawa matakan gwamnatocin wanda kuma ya zo kimanin watanni biyar - kafin ƙasar ta gudanar da zaɓukan shugaban ƙasa dana majalisun dokoki da kuma na gwamnoni.

Babban Akawun gwamnatin tarayyar Nijeriya Alhaji Ibrahim Ɗankwambo ya ce ƙasar ta rarraba kuɗin da yawan sa yakai Naira miliyan dubu 404, da kuma miliyan 270, wato ƙwatankwacin dalar Amirka miliyan dubu biyu da miliyan 700, da kuma wasu dala miliyan dubu biyu daga asusun ajiyar rarar man fetur nata.

A al'adar Nijeriya dai gwamnati na yawaita fitar da kuɗi da sunan yin aiki a shekarun yin zaɓuka, abinda ya sa masu nazari ke dasa ayar tambaya game da ingancin kashe kuɗin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala