1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Katar ta hana Saudiya jigilar alhazanta

Ramatu Garba Baba
August 20, 2017

Kasar Saudiya ta ce mahukuntan kasar Katar sun hanata dauko maniyata bayan da Katar din ta hana jiragen Saudiya sauka a filin jirgin saman kasar da ke Doha.

https://p.dw.com/p/2iX9p
Saudi-Arabien Mekka Hajj Pilger umrunden die Kaaba
Hoto: Getty Images/AFP/A. Gharabli

Kasar Saudiya ta ce mahukuntan kasar Katar sun hana ta dauko maniyata bayan da Katar ta hana  jiragen Saudiya sauka a filin jirgin saman kasar da ke Doha. Daraktan kamfanin sufurin jiragen sama na Saudiya Saleh al-Jasser ya ce ya zuwa wannan lokacin babu jirgin da ya dauko maniyyata kamar yadda aka shirya da mahukuntan kasar.

Wannan dai ba ya rasa nasaba da takaddamar da ke a tsakanin kasashen biyu bayan da Saudiya da wasu kasashen larabawa suka sanar da yanke hulda da kasar ta Katar bisa zargin ta da taimakawa ayyukan kungiyar IS