1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka zata hada kai da kasar Rasha

February 16, 2017

Dangantakar Amirka da Rasha ta mamaye taron G20.

https://p.dw.com/p/2XirL
Donald Trump und Wladimir Putin
Hoto: picture alliance/A. Lohr-Jones/A. Astafyev/CNP POOL/Sputnik/dpa

Sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya ce Amirka za ta hada kai da kasar Rasha kan duk wasu harkoki da Amirka zata amfana da su, a dai dai lokacin kuma da Moscow ke matsawa gwamnatin shugaban Donald Trump lamba dangane da alkawuran kyautata kawancensu da suka cimma. Wadannan bayanan dai sun fito ne bayan ganawar farko da Mr. Tillerson da takwaransa na kasar Rasha Sergei Lavrov lokacin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 masu karfin arziki da ake yi a nan Bonn.

Mr. Lavrov ya shaidawa ministan na Amirka Mr. Rex cewar ba za a warware dukkanin bukatu ba, sai dai bangarorin biyu za su iya fahimtar juna ne a fannonin da bukatu suka kama. Ministan na Amirka dai ya kasance a taron na G20 ne a matsayin babban jami'in diflomasiyyan Amirka, a dai dai kuma lokacin da shugaba Trump ke nuna cewa burin Amirka ne Amirka ta daura sama komi.