1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawancen jamíyun yan shiá a Iraqi sun sake zabar Jaáfari ya jagoranci sabuwar gwamnati.

February 13, 2006
https://p.dw.com/p/Bv8F

Jamiíyun kawancen yan Shiá dake mulkin kasar Iraqi sun sake zabar Ibrahim Jaáfari domin jagorantar sabuwar gwamnatin da zaá nada. Ibrahim al-Jaáfari ya kada abokin takarar sa kuma mataimakin shugaban kasar Adel Abdul Mahdi da kuriá daya tilo. A yau ne kuma ake cigaba da shariár tsohon shugaban kasar Iraqin Saddam Hussaini, lauyoyin dake kare shi sun musanta rade radin cewa Saddam din zai shiga yajin cin abinci, sai dai sun baiyana cewa Saddam zai kauracewa kotun har sai an sake sabon alkalin kotun Raúf Rashid Abdulrahman.