1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kawancen mulki a Jamus ya shiga garari

Yusuf BalaSeptember 19, 2016

Zaben da aka yi na yanki a birnin Berlin na nan Jamus a karshen mako, ya nuni da cewa ci gaban kawance tsakanin jam’iyyar CDU mai mulki da SPD ba mai yiwuwa ba ne a hasashen masana.

https://p.dw.com/p/1K4xq
Deutschland Merkel und Gabriel PK im Bundeskanzleramt zur Griechenland-Krise
Kawancen na SPD ta Gabriel da CDU ta Shugabar gwamnati Merkel da kamar wuya a 2017Hoto: Reuters/F. Bensch

Bayan da jam'iyyar ta Social Democrats (SPD) da jam'iyyar ta Shugabar gwamnati Merkel Christian Democratic Party (CDU) suka bayyana da zama jam'iyyu biyu mafiya karfi, dukkaninsu sun ga koma baya tun bayan yakin duniya inda suka ga sakamako mafi muni a zaben babban birnin kasar ta Jamus. Abin da ke nufin ba za su iya ci gaba da gwamantin hadaka ba, lamarin da Hans Joachim Funke, masanin siyasa a Jamus ya bayyana da zama annoba:

"Wannan na nufin watsi da hadaka babba ta jam'iyyun mutane biyu CDU da SPD a Berlin, wannan annoba ce da ka iya jawo koma baya a harkokin zamantakewa da tattalin arziki da ma harkokin da suka shafi shugabanci".

Jam'iyyar Social Democratic Party ko (SPD) ta samu kashi 21.6 cikin dari na kuri'un da aka kada, abin da ke nuna cewa za ta iya neman kawance dan samun shugabanci daga jama'iyyar Greens da Left Party.Tuni dai Michael Müller na SPD kuma magajin garin na birnin Berlinn ya nuna cewa a shirye yake ya fara tattaunawa da dukkanin jam'iyyun baya ga jam'iyyar AfD mai adawa da baki, amma hakan shi ke zama zabi idan ta gagara da jam'iyyar Greens da Left Party.

Berlin Wahlen zum Abgeordnetenhaus Michael Müller
Michael Müller magajin garin birnin BerlinHoto: picture-alliance/dpa/B. von Jutrczenka

Shi kuwa jagoran na SPD Sigmar Gabriel ya ce birnin na Berlin ya tsaya kan tafiya da kowa da adalci.

"Tabbas wannan shi ne sakamako ina nufin abin da Mueller ya bayyana gaskiya ne wannan na nufin mutane da ke ganinmu daga nesa muna tare, mun yi waje da masu adawa da baki, idan muka hada kai siyasarmu za ta kara karfi, abin da kuma zai zama alheri ga Jamus."

Dan takara daga jam'iyyar ta CDU Frank Henkel ya ce sun koyi darasi:

Infografik Abgeordnetenhauswahl Berlin 2016 Englisch
Sakamakon zabe na Berlin

"Masu kada kuri'a sun jaddada mana darasi, dukkanin jam'iyyun SPD da CDU mun sha kasa idan aka kwatanta da shekarar 2011. A namu bangren na CDU wannan shi ne sakamako, ba zamu yaudari kanmu ba wannan ba abin da zamu ce mun gamsu da shi ba ne".

Dukkanin jam'iyyun dai sun ga wannan zabe a matsayin makomar zaben shekara mai zuwa a matakin tarayya, inda Gabriel ya ce hadin kai na jam'iyyu shi ne za su ba wa fifiko yanzu, sannan su tura 'yan takara kadan a gaba dan su sami nasara, sabanin abin da suka yi a shekarar 2013.