1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenia Kufour

Mohammed, ZainabJanuary 10, 2008

An kasa cimma matsaya tsakanin gwamnatin Kibaki da 'yan adawa a Kenya

https://p.dw.com/p/Cnuh
Kofi AnnanHoto: AP

'yan adawan ƙasar ƙenya sun bayyana cewar sakamakon gaza cimma kawo ƙarshen saɓani akan zaɓen shugaban kasa,tsohon Sakatare General na Majalisar Ɗunkin Duniya Kofi Annan ya amince da ɗaukar nauyin shiga tsakanin ɓangarorin biyu.

Babban Sakatare na jami'iyyar adawa ta ODM dake Kenya Anyang Nyongo,ya bayyana nadamarsa dangane da rushewan tattaunawar da shugaban Ghana John Kufuor ya jagoranta a kokarin warware wannan rikici na siyasa.

Bayan kwanaki biyu na ziyarar shiga tsakani  a Kenyan dai yau ne shugaban na ƙungiyar gamayyar Afrika Kofour ya bar Kenya.Sanarwar sakamakon bayan ziyarar tasa na nuni dacewar,ya samu amincewar shugaba Mwai Kibaki da shugaban  adawa Raila Odinga,na aiki tare da kwarraun shugabannin Afrika akarkashin jagorancin Kofi Annan,domin cimm warware takaddamar data dabaibaye zaɓen shugaban ƙasa na ranar 27 ga watan Disamba a Kenyan.

Shugaba Joaquim Chissano na ƙasar Mozambique na ɗaya daga cikin shugabbanin Afrika da suka ziyarci kenyan domin sasanta wannan rikici..Yace yanzu dai babu wani tudun dafawa da muka cimma a warware wannan rikici sai dai muna fatan samar da wasu hanyoyi na gano bakin zaren warware shi,ana iya cewar da sauran lokaci kuma zamu sake hadewa, kamar yadda muka haɗu da sauran shugabbanin Afrika uku, akarkashin jagorancin shugaban Ghana"

Masu sa ido na ƙasashen ketare a zaɓen  dai sun shaidar dacewar an tabka magudi.A sakamakon haka ne rigingimu suka ɓarke a sassa daban na Kenya,wanda ya kashe akalla mutane 500,bayan dubbai da suka kaurae daga matsugunnensu.

A yanzu haka dai hukumomin bada agaji da suka hadar da na Majalisar Ɗunkin Duniya na cigaba da kai agajin abinci wa dubbannin mutane da suka tsere daga matsugunnensu a wannan rikici na Kenya kamar yadda kakak8in ƙungiyar tallafin Abinci ta Majalisar dunkin duniya a Kenya,Peter Smerdon ya bayyanna.."Abunda ƙungiyar WFP takeyi shine rarraba kayayyakin abinci masu gina jiki da mutane ke bukata da suka haɗar da wake da masara da makamantan su,domin gwamnatin kenyan ta taimakawa kungiyar Red Cross da kayayyakin abinci,wanda kawo yanzu an rarraba mutane dubu 60 daga cikin dubu 100 da aka kiyasta cewar sun kaurace daga matsugunnensu dake areawaci da kuma yammacin Kasar,sai dai lamura sun fara lafawa"

A wannan ziyara tasa ta shiga tsakani dai shugaba Kufour ya gana a lokuta daban daban shugabannin biyu,inda ya faɗawa manema labaru kafin kama hanyarsa cewar,abu mafi muhimmanci game da wannan taron shine koda shike baa cimma warware rikicin siyasar ba,dukkanin ɓangarorin biyu sun amince da kawo karshen rigingimu dake addabar ƙasar.