1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kevin Rudd ya lashe zaɓen majalisar dokoki a Australiya

November 25, 2007
https://p.dw.com/p/CSrm
Kevin Rudd zai zama sabon firaministan ƙasar Australiya bayan da jam´iyarsa ta Labour ta ka da jam´iyar masu sassaucin ra´ayi Liberal ƙarƙashin jagorancin firaminista mai ci John Howard a zaɓen ´yan majalisar dokokin ƙasar. Jam´iyar ta Labour ta samu kashi 53 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kaɗa idan aka kwatanta da kashi 46 cikin 100 da ƙawancen jam´iyun Liberal da ta masu kishin ƙasa suka samu. Rudd dan shekaru 50, tsohon jami´in diplomasiyan Australiya ne, yayi alƙawarin saka ƙasar kan abin da ya kira wata turba ´yanci wajen tsara manufofinta na ƙetare. Ya kuma sha alwashin janye sojojin Australiya 500 daga Iraqi sannan ya ce zai rattaba hannu kan yarjejeniyar birnin Kyoto. A cikin mako mai zuwa za´a rantsad da shi a matsayin sabon firaminista.