1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ki ki ka ka a harkokin zaben shugaban kasa a Haiti

February 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7t

Jami´an diplomasiyya a kasar Haiti, na nan na tunanin matakan daya kamata su dauka don tabbatarwa da Mr Rene Preval nasasar da yake ikirarin ya samu, a zaben shugaban kasa da aka gudanar.

Da alama dai kokarin daukar wannan matakin ya samo asali ne don kaucewa kara shiga rudanin siyasa, da gudanar da zagaye na biyu na zaben ka iya jawowa.

Daga cikin matakan da jami´an ke tunanin dauka kuwa akwai batu na janye wasu kuri´un zabe sama da dubu tamanin wadanda babu komai a jikin su.

Yin hakan a cewar su ka iya daga nasasar ta Mr Rene Preval daga kashi 48 da digo 7 cikin dari izuwa kashi 51 cikin dari, wanda hakan ka iya bashi nasasar lashe zaben ba tare da an gudanar da wani sabon zaben na zagaye na biyu ba..