1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kiki ka kan da ake ciki sakamakon rahoton Mdd akan Rafik Hariri

Ibrahim SaniNovember 23, 2005

Mdd ta bukaci kasar Syria daga daina kawo cikas game da kokarin da ake na gano musabbabbin tashin bom din daya halaka Rafik Hariri, tsohon Faraministan kasar Lebanon

https://p.dw.com/p/Bu3z
Detlev Mehlis
Detlev MehlisHoto: AP

Jakadan Amurka na musanman a Mdd, John Bolton ya bukaci Syria cikin gaggawa data daina kawo cikas game da binciken da Mdd keyi na sanin musabbabin rasuwar tsohon Faraministan Lebanon, wato Rafik Hariri da wasu mutane sama da dozin daya.

Da alama dai wannan kira yazo ne a daidai lokacin da mahukuntan na Syria suka bukaci taimakon babban magatakardar Mdd, wato Kofi Anan na warware sabanin dake tsakanin su da shugaban tawagar binciken na Mdd, wato Detlev Mehlis.

Wannan dai sabani a cewar bayanai da suka iso mana nada nasaba ne da gurin da za a zauna don sauraren wadanda ake tuhumar guda shida, wadanda dukkannin su manya manyan jami´in gwamnatin kasar ne ta Syria,ba a da bayan haka akwai kuma sanin irin tambayoyin da za a yi musu a lokacin wannan zama.

Rahotanni daga kasar sun shaidar da cewa, Mehlis na son a gudanar da wannan binciken ne a kasar Labanon, wanda kuma mahukuntan na Syria suka ce akwai hatsari dangane da hakan a don haka akwai bukatar a sake gurin zama.

Idan dai za a iya tunawa a wani dan kwarya kwaryan rahoto a watan daya gabata, Mr Mehlis ya nunar da cewa yana da gamsashiyar shaida dake nuni da cewa akwai sa hannun wasu jamian daga kasashen Syria da Labanon a tahin bom din da yayi sanadiyyar rasuwar tsohon Faraministan kasar ta Labanon, wato Rafik Haririn da ragowar mutanen sama da dozin daya.

Kafin dai fitowar wannan rahoto, mahukuntan na Syria ba sau daya ba ba sau biyu ba sun karya wannan zargi da ake musu da cewa bashi da tushe balle makama.

Game kuwa da fitowar wannan rahoto da kuma kokarin da Mdd keyi na ganin an gano masu laifi don hukunta su kamar yadda doka ta tanadar, tuni majalisar ta bukaci kasar Syria ba tare da bata wani lokaci ba data bawa wadan nan jami´ai goyon bayan da suke bukata wajen gudanar da wannan bincike.

Game kuwa da bukatar da kasar ta Syria ta nema daga sakataren na Mdd, jakadan kasar Amurka a Majalisar, wato John Bolton cewa yayi kasar ta Syria tayi hakan ne don haifar da tafiyar hawainiya a game da kokarin da ake na binciko hakikanin gaskiya game da tashin bom din daya halaka Mr Rafik Haririn.

Bisa hakan Mr Bolton, yace akwai bukatar mahukuntan na Syria bada goyon bayan da ake bukata don ganin cewa Mr Mehlis ya samu cimma burin da kwamitin sa yasa a gaba,kafin karewar wa´adin da aka bashi na 15 ga watan disamba na wannan shekara da muke ciki.

Ya zuwa yanzu dai Sakataren Mdd Kofi Anan na nan naci gaba da kokarin ganin cewa an samu bakin zaren warware wannan takaddama data taso a tsakanin mahukuntan na Syria da kuma masu gudanar da binciken, don ganin cewa komai ya tafi dai dai wadaida ba tare da fuskantar wani cikas ba.