1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kimanin mutane miliyan191 ke gudun hijira a duniya

April 6, 2006

Nahiyar Turai ke karbar bakuncin kashi daya bisa uku na 'yan kaka-gida a duniya

https://p.dw.com/p/Bu0n

Kasashe masu ci gaban masana’antu zasu samu bunkasar yawan jama’a a cikin shekaru goma masu zuwa ne sakamakon ‘yan gudun hijira dake kaka-gida a cikinsu. Wannan maganar musamman ta fi shafar kasashen Turai. Domin kuwa kasashen na bukatar ‘yan kaka-gida in ji Rita Süssmuth, wadda ta gabatar da rahoton MDDr akan bunkasar jama’a a birnin New York, ta kuma kara da cewar:

“Yawa-yawancin mutane sun dauka ne cewar ‘yan gudun hijira mutane ne dake tuttudowa zuwa kasashe mawadata saboda matsaloli na talauci da rashin wata kyakkyawar makoma a kasashensu. Amma fa a daya bangaren muma muna bukatarsu ruwa a jallo.”

A sakamakon koma-bayan haifuwar da ake fuskanta a kasashe mawadata, wadannan ‘yan gudun hijira ke cike gibin da kasashen ke fama da shi wajen bunkasar al’umarsu. A cikin bayanin da kwararru na MDD suka yi sun yi nuni da cewar in har an ci gaba da samun kwararar ‘yan gudun hijira daga kasashe matalauta zuwa kasashe masu ci gaban masana’antu kamar yadda lamarin yake a yanzu hakan zai taimaka kasashen su samu bunkasar al’uma iya gwargwado daga shekara ta 2010 zuwa shekara ta 2030. Rita Süssmuth ta ce ba wai kawai saboda bunkasar jama’a ne ake bukatar ‘yan kaka-gidan ba. Kazalika lamarin na da nasaba da manufofi na tattalin arziki saboda wadannan ‘yan gudun hijira su kan kama ire-iren ayyukan nan da wasu ke kyamarsu.

A baya ga nahiyar Turai dake da kashi daya bisa uku na yawan ‘yan gudun hijira su kimanin miliyan 191 dake kaka-gida a sassa daban-daban na duniya suma kasashen arewacin Amurka na da dimbim ‘yan kaka-gida, inda yawansu a yanzu haka ya kai miliyan 44 da dubu 500. Kazalika kasashe irinsu Australiya da New Zealand da Japan duk kasashe ne da ‘yan gudun hijira ke sha’awar yin kaka-gida a cikinsu.

A nasa bangaren ministan cikin gida na kasar Ghana Papa Owusu-Ankomoah ya bayyana damurasa a game da ci gaban da ake samu inda dubban matasa na Afurka ke sadaukar da ransu a kokarinsu na neman shigowa nahiyar Turai, inda ya kara da cewar:

“A matsayina na dan Afurka wannan maganar tana ci mini tuwo a kwarya, musamman ma ganin yadda wadannan mutane ke sadaukar da kansu domin shigowa Turai ko ta halin kaka.”

Papa Owusu-Ankomoah dai ya ce duk da haka wadannan ‘yan gudun hijira zasu iya taka muhimmiyar rawa a manufofi na raya kasa da magance matsaloli na talauci, musamman idan an dauki nagartattun matakai na kyautata alakarsu da kasashensu na asali, kamar yadda Ghana ke yi yanzu haka inda take kokarin ba wa ‘yan kasar dake kaka-gida a ketare damar kada kuri’a lokacin zabe da kuma neman shawo kansu wajen dawowa gida domin a ci amfaninsu.