1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kira ga dage zaben shugaban kasa a Burundi

Gazali Abdou TasawaJuly 6, 2015

Taron shugabannin ƙasashen gabashin Afrika ya yi kira da a ɗage zaɓen shugaban ƙasar Burundi na 15 ga wannan wata na Yuli zuwa 30 ga watan

https://p.dw.com/p/1FtiY
Konferenz in Kampala
Hoto: AP

Shugabannin ƙasashen gabashin Afirka sun yi kira da a ɗage zaɓen shugaban ƙasar Burundi har ya zuwa ranar 30 ga wannan wata na Yuli da muke ciki.Sun bayyana haka ne a lokacin wani taron koli da ƙungiyar ƙasahen gabashin Afirka ta shirya a yau a ƙasar Tanzaniya a wani yinƙuri na neman shawo kan rikicin siyasar ƙasar Burundi.

Sai dai mafi yawancin shugabannin ƙasashen yankin ba su halarci taron ba wanda shugaban ƙasar ta Tanzaniya da takwaransa na ƙasar Yuganda ka dai suka halarta,a yayin da Shugaba Paul Kagame na ƙasar Ruwanda da Uhuru Kenyatta na ƙasar Kenya dama Pierre N'Kurunziza na ƙasar ta Burundi suka wakilto wasu ministocinsu kawai zuwa taron.