1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kirismeti a kasashen larabawa

December 23, 2005

Duk kiristoci dai na bikin kirismeti a ko'ina inda suke. Sai dai bikin ya bambanta ne daga kasa zuwa zuwa kasa, da kuma ko wace #arika kiristocin ke bi. Kiristocin kasashen larabawa ma na gudanad da wannan bikin a kasashensu, duk da cewa dai, a kusan duk kasashen, muslmi ne suka fi yawa.

https://p.dw.com/p/BvU7
Shagulgulan bikin kirismeti a kasar Lebanon.
Shagulgulan bikin kirismeti a kasar Lebanon.Hoto: AP

A kusan duk kasashen larabawa dai, akwai musulmi da kirista da ke zaman cude ni in cude ka da juna cikin lumana. Saboda haka ma, a lokacin bukuwansu na addini kamar dai na sallah ko kuma na kirismeti, sai ka ga kusan duk jama’a ne ke yinsu gaba daya, ba tare da yin la’akari da ko bikin wane addini ba ne. Kamar yadda Yuhaina wata kirista ta kasar Lebanon ta bayyanar:-

„Ana fara shirye-shiryen bikin kirismeti ne tun wata daya kafin ranar bikin. Za ka ga ko’ina, ana ta yi wa shaguna da gidaje ado, an sanya musu fitilu masu kyalli daban-daban daddare; a kan tituna da makarantu kuma, za a iya gani ko kuma jin mutane suna ta wakar kirismeti. Kiristoci dai sun fi murnar zuwan wannan lokacin. Amma ba kiristocin kawai ne ke yi wa gidajensu ado ba. Muslmin ma na yin haka.“

A kasar Masar ma, inda mafi yawan al’ummanta muslmi ne, kiristocin kasar na bikinsu na kirismeti. Tun shekaru 2 da suka wuce ne ma aka mai da ranar 7 ga watan Janairu, ranar hutun kirismeti a hukumance; saboda a can, kiristocin mabiya darikar Orthodox ne, wadanda kalandarsu ta bambanta da na kiristocin yamma, masu amfani da kalandar darikar katolika. Rita, wata kiristar darikar Orthodox ce a kasar Masar. Ga yadda dai ta ce suna gudanad da bikinsu na kirismeti:-

„A galibi duk iyalinmu na taruwa ne a gu daya a wannan lokacin. Baffana, da kanni da yayyanina da `ya`yansu, da kakata, dukkansu su kann zo gidanmu don yin bikin kirismeti. A nan Masar dai, ana dafa abinci da yawa a lokacin kirismeti. Mu talotalo muke yankawa. Matasa kuma, sai su fita waje su je suna ta shagulgulansu na bikin. Ana dai shirya bukukuwa da dama kamarsu raye-raye da sauransu. A jajiberen kirismetin, mafi yawan kiristocin Masar su kan je coci don halartar taron ibada, dauke da azumi. Sai bayan sun yi ibada, sun yi addu’o’i ne suke dawowa gida su karya azumin.“

A kasashen yankin Golf, inda babu kiristoci da yawa, lamarin daban yake da kasashen Masar ko Lebanon. A kasar Saudiyya alal misali, ba a bukukuwan kirismeti, sai dai a ji labarinsu a kafofin yada labarai. Wani dan kasar Osam, ya bayyana cewa:-

„A Saudi Arebiya dai ba a san kirismeti ba. Hakan kuwa na da dalilai ne guda biyu. Na farko, saboda masu yin wannan bikin ma, a cikin gidajensu kawai suke yi, ba tare da wani na waje ya san abin da suke ciki ba. Na biyu kuma, saboda doka ta hana yin bukukuwan kiristoci kamarsu kirismeti ko sabuwar shekara a bayyane, kamar a otel alal misali. Mabiya wasu addinai za su iya yin bukukuwansu, amma a bayan shinge, ko kuma a ofisoshin jakadancinsu.“

A kasar Dubai kuma, wadda ke bin alkiblar kasashen yamma, ana bikin kirismetin da sabuwar shekara, ba tare da wani shinge ba. Nayla Nasser, wata `yar kasar ce ma’aikaciya, kuma musulma. Amma ta ce tana halartar bukukuwan sabuwar shekara, kamar dai yadda duk sauran al’umman kasar da muslumi da wadanda ba musulmi ba ke yi.

Bisa cewarta dai:-

„A Hadaddiyar Daular Larabawa, bam u san wani bambanci ba. Duk jama’a na da cikakken `yancinsu. Za su iya yin bukukuwansu a cikin gidajensu ko kuma a bayyane. Kiristoci na iya tafiyad da harkokin addininsu kamar yadda suka ga dama. A otel-otel ma ana iya ganin itatuwan kirismeti da ake kakkafawa a wannan lokacin, saboda akwai baki da yawa da ke aiki a nan. A wasu lokutan ma, shugabannin kamfanoni na rarraba wa ma’aikatansu kyaututtuka kamarsu na mutum mutumin kirismeti da aka yi da cakula“.