1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kirkiro na'urar taya jami'an kan hanya bincike a Najeriya

Yusuf Ibrahim Jargaba/GATAugust 31, 2016

A Najeriya wani matashi a jihar Katsina ya kirkiro wata na'ura da jami'an tsaro masu bincike kan hanya kamar 'yan sanda su iya yin amfani da ita wajen banbace wa direbobi wuraren bincike na gaske da kuma na boge

https://p.dw.com/p/1Jt5H
Nigeria Sicherheitskräfte Kampf gegen Boko Haram
Hoto: Getty Images/AFP/Q. Leboucher

Wani matashi a jihar Katsinar tarayyar Nigeria ya kirkiro wata na'ura da jami'an tsaro masu bincike kan hanya za kamar 'yan sanda ko NDLEA, ko immagration su iya yin amfani da ita wajen banbace wa direbobi wuraren bincike na gaske da kuma irin na boge da barayi ko sauran bata gari ke kafawa kan tituna.

Ita dai wannan na'ura tana amfani da hasken rana. Jami'an tsaro za su iya amfani da ita amaddain kunna wuta a bakin titi wanda bata gari ma kan iya yin hakan dan muzguna jama'a. Sanusi Gambo shi ne wanda ya kirkiri wannan na'urar ya bayyana dalilansa na kirkiro da ita:

Grenze Nigeria Kontrolle
Hoto: Natasha Burley/AFP/Getty Images

"Babban dalilin dai shi ne kamar za ka ga cewa akasarin direbobi masu tafiya bisa hanya, wata sa'a za ka ga an tsaida su, kuma da fitilar hannu ake tsaida su, kuma so tari sai sun matse wa mutanen da suka tsaida su din suke ganewa cewa ba jami'an tsaro ba ne, bata gari ne kawai.To duk inda ka hango fitila a wurin bincike mai makon ka koma da baya a bisa tsoron ko barayi ne, zaka tabbatar da cewa wadannan jami'an 'yan sanda ne"

Shin ko ta yaya direba zai iya gane cewa jami'an tsaro ne kan titi? Gambo ya yi karin bayani:

" Ko wane wurin binciken yana da namba, kuma an rubuta suna jami'in da ke wurin, ko dan sanda, ko immagration ko kwastam a sama. Sannan kuma in hanya a tsaye take , to za ka iya hango hasken abin tun a kilomita biyu kafin ka iso a wurin. Kuma an rigaya an yi masa doka cewar wasu ba za su kirkiri wannan na'urar ba sabili da a nan aka yi ta."


Sai dai Gambo ya bukaci mahukunta da su rika karfafa ma mutane masu fasaha gwiwa dan kara samun cigaba.kuma direbobin mota masu aikin jigila sun bayyana gamsuwarsu da wnnan na'ura kamar dai yadda wannan daya daga cikinsu ke cewa.

Nigeria Symbolbild Korruption
Hoto: picture alliance/NurPhoto

" Wannan na'ura za ta taimaka wa al'umma masu amfani da motoci bisa hanya sosai musamman game da barazanar barayi da sauran bata gari masu fashi bisa hanya"

A Nigeria dai Masu ababen hawa kan sha gamuwa da barazana iri-iri daga bata gari da sunan jami'an tsaro ta hanyar kunna wuta a bakin titi.