1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koda wukaken yaki tsakanin Habasha da Eritera

Yahouza SadissouNovember 3, 2005

Majalisar Dinkin Dunia ta bayyana damuwa a game da yiwuwar sake barkewar yaki tsakanin Habasha da Eritrea

https://p.dw.com/p/Bu4U

Majalisar Dinkin Dunia ta nuna damuwa a game da yiwuwar sake barkewar saban yaki tsakanin kasashe Habasha da Erytrea masu makwabtaka da juna.

Sakataran Majalisar Koffi Annan ya bayyana samun cikkakun labarai masu nuna shirye shiryen da kasashen 2 ke yi na komawa fagen daga, bayan yarjejeniyar zaman lahia da su ka cimma, bisa jagorancin Majalisar dinkin Dunia, a shekara ta 2000 a kasar Algeria.

A game da haka Annan ,ya jaddada kira ga hukumomin kasashen 2, da su yi anfani da wannan yarjenejiya , ta hanyar kawce kasashen su da al´ummomin su, daga wani saban yaki.

An yi shekaru a na kafsawa tsakanin dakarun Ethiopia da na Erytrea, wanda a sakamakon sa, mutane kimanin dubu 80, su ka rasa rayuka, da dama kuma su ka shiga uwa dunia.

A shekara ta 2000, Majalisar Dinkin Dunia, ta gayyaci kasashen zuwa taron sulhu, waanda a sakamakon sa a ka samu nasara tsagaita wuta.

Tawagogin kasashen sun yi alkawarin amincewa da girka wata hukuma ta mussaman da za ta shata iyakokin tsakanin Erytrea da Habasha biosa sa idon Majalisar Dinkin Dunia.

A hannu daya kuma Majalisar ta amince ta kai sdakarun shiga tsakani domin tabatar da wanzuwar yarjejeniyar da aka cimma.

Wannan hukuma ta gabatar da sakamakon binciken da ta gudanar a shekara ta 2002,to saidai har ya zuwa yanzu hukumomin Addis Ababa, sun ki amincewa da shi, abinda ya jawo jinkiri ga fara hurta iyakokin.

A nata gefe kasar Eritrea, ta bayyana barazanar sake barkewar yaki muddun Habasha ta ci gaba da watsi da sakamakon rahoton da hukumar ta gabatar.

Koffi Annan ya yi kira ga hukumomin Majalisar Dunia, da su yi iya kokarin su, don ganin Habasha da Eryitrea sun tabatar da zaman lahia tsakanin su ta hanyar anfani da yarjejeniyar ad su ka sa hannu a kai.

Shugaban komitin sulhu na Majalisar dinkin dunia, ambassada Andrei Denisov na kasar rasha, ya gabatar da rahoton da shugaban rundunar shiga tsakani na yankin ya shirya wanda ko shaka babu ke tabatar da manufofin da shirye shiryen kasashen na komawa yake yake.

Ambassada Andrei ya bayyana cewa, a yanzu haka komitin Sulhu na cikin tantanawa a kan matakan ciwon kan kasashen 2 na kwance damara yaki.

Kazalika, su na masu tantanawa, tare da wakillan kasashen a kan mahimancin cika alkawuran da su ka dauka, na amincewa da rahoton hukumar hurta iyaka tsakanin su.