1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koffi Annan ya buƙaci Libanon ta kwance ɗamara yaƙin Hizbullahi

October 20, 2006
https://p.dw.com/p/BufE

Sakatare Jannar na MDD Koffi Annan, yayi kira ga hukumomin ƙasar Libanon, su cika alƙwarin da su ka ɗauka, na kwance ɗamara yan Hizbullahi, bayan yaƙin da aka gwabza tsakanin wannan ƙungiyar yan schi´a, da Isra´la a watannin da su ka gabata.

A cikin rahoton da ya miƙawa komitin Sulhu na MDD, Annan, ya bayyana bukatar ganin Hizbullahi, ta aje makamai, ta kuma rikiɗa zuwa jam´iyar siyasa, wace za a dama da irta a harakokin mulkin ƙasar Libanon.

Sannan, ya bayyana burin kyauttata hulɗoɗin diplomatia, tsakanin Syria, da Libanon ,ta hanyar shata iyaka tsakanin su, ba tare da an kai ruwa rana ba.

Rahoton na Koffi Annan, yayi bitar halin da ake ciki, a ƙasar Libanon, tun bayan ƙudurin da MDD ta ɗauka, na hidda rundunonin ƙasashen ƙetare, mussamman na Syria daga wannan ƙasa.

Ya ce duk da mtasaloli iri iri da ake fuskanta, an cimma nasara, kyakyawa, saidai har yanzu, da sauran rina kaba, wajen samar da cikkaken yanci ga Libanaon.