1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koizumi ya kai ziyara a Ethiopia

May 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv03

Praministan ƙasar Japon, Yunichiro Koizumi, na ci gaba da ziyara aiki a ƙasar Ethiopia.

Bayan ganawar da yayi jiya,da Praminista Meles Zenawi , Koizumi ,ya bayyana wa manema labarai, mihimman batutuwan da su ka tantana.

Wannan batutuwa sun shafi, bukatar Japon, ta samun kujerar dindindin, a komirtin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Kazalika, ya bayyana goyan baya, ga ƙasashen Afrika, na samun wakilai a wanan komiti.

Nan gaba a yau, zai gana da magabatan ƙungiyar taraya Afrika, inda za su tantana wannan batu.