1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokakin inganta harkokin tsaro a Afghanistan

September 29, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9s

Shugaba Hamid Kharzai na Afghanistan yace a shirye yake ya tattauna kai tsaye da shugabannin yan tawaye na kasar.Mr Kharzai yace ya dauki wannan matakin ne, a kokarin da gwamnatin sa keyi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, a fadin kasar baki daya. Bugu da kari, Mr Kharzai ya kuma kalubalanci shuwagabannin kungiyoyi masu fito na fito da gwamnati dasu tsaya takara a zaben gama gari da ake shirin yi a kasar a nan gaba.Har ila yau shugaban na Afghanistan yayi alkawarin bawa shuwagabannin ire iren wadannan kungiyoyi mukamai, matukar suka ajiye makaman su.Mr Hamid Kharzai ya fadi hakan ne kuwa awowi kadan bayan wani dankunar bakin wake ya tashi bom din dake jikinsa, inda nan take mutane 30 suka rasa rayukan su, bayan wasu da dama sun jikkata.Tuni dai yan kungiyyar Taliban, suka yi ikirarin hannun su a cikin tashin wannan bom.Tuni shugaban na Afghanistan yayi Allah wadai da wadanda ke da hannu a cikin wannan hari:

Mr Kharzai yace mutumin daya kira kansa a matsayin musulmi na kwarai, ba zai yiwu ya kai hari kann mutanen da basu ji basu gani ba. Yace ire iren wadannan mutane makiya ne ga Afghanistan da kuma Al´umma.