1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin ceto miliyoyin mutane daga matsalar rashin ilimi

Issoufou Mamane/ MNASeptember 9, 2015

Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da mayar da hankali ga samun mafita ga mutanen da ba su iya rubuta da karatu a duniya ba.

https://p.dw.com/p/1GTct
Burundi Schule in Bujumbura
Hoto: picture-alliance/dpa/T. Schulze

Ganin yadda har yanzu haka a duniya akwai miliyoyin mutanen da ba su iya rubutu da karatu ba, Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar 8 ga watan Satumba matsayin ranar yaki da jahilci inda ake mayar da hankali ga ceto miliyoyin mutane daga masifar jahilci.

Kasashe masu tasowa su ne suka fi fama da matsalar yawan wadanda ba su iya rubutu da karatu ba. Alal misali a Jamhuriyar Nijar, sama da kashi 21 cikin 100 na mata 'yan kasa da shekaru 15 zuwa 29 kacal suka samu horon yaki da jahilci a cikin harsunan kasar irin su Hausa da Zabarmanci da Fulanci ko kuma Buzanci da ma wasu harsunan kasar.

Südafrika Astrid Lindgren Memorial Award 2015 für PRAESA
Yaki da jahilci a unguwannin marasa galihu a Afirka ta KuduHoto: cc-by/Astrid Lindgren Memorial Award

Da dama ne daga cikin jama'ar kasar ke amfani da harsunan da suka koya domin inganta harkokinsu na yau da kullum wato kamar kasuwancinsu, ko kuma amfani da salula da sauran na'urorin zamani.

Ilimi madogarar kyautata rayuwa

Sama da shekaru 30 ke nan da hukumomin kasar ta Nijar suka kadamar da tsarin ceto 'yan kasar da ba su samu nasarar shiga karatun arabiya ko na boko ba ta hanyar kafa makarantun yaki da jahilci a cikin harsunan kasar daban-daban a wani matakin kawar da jahilci daga kasar kamar yadda Malam Issa Basharu jami'i a ma'aikatar da ke kula da ilimi a birnin Tawa ke cewa:

"Malamai sama da 2000 aka koyar a fannin yaki da jahilci, a cikinsu kuna kwai mata 1940. Akwai cibiyoyi guda 70, za a kuma kara wasu cibiyoyi 10 musamman ga yara da ba su shiga makarantun boko ba. Tuni ma dai wadannan cibiyoyin suka fara aiki."

Amfanin yaki da jahilci

Wannan ya sa da dama daga cikin wadanda ba su yi karatun bokon ba ko na arabiya suka maida hankali ga koyon karatun da rubutu a cikin harsunansu, inji Dillo Yahaya :

"Na yi yaki da jahilci ga shi kuma ina cin amfanin shi cikin kasuwancin da nake yi. Ban yi makaratun arabiya da boko ba, har kudi na kashe domin in yaki jahilci, to ga shi ina cin amfanin abi na."

Hörsaal in der Uni Goma
Ilimi ga manya a garin Goma na KwangoHoto: DW/S. Schlindwein

Shi ko Maman Sani Abdulsalam, bayani ya yi na irin moriyar da ya ke ci yanzu haka sakamakon karatun harshen hausa da ya yi:

"Ina cin moriyarshi kamar wanda yayi makarantar boko ya samu aiki yana ciyar da kanshi da kuma iyalinshi. Ni ma haka nan ne nake yi, saboda ina aiki a wata tashar radiyo mai zaman kanta, albarkacin karatun da na yi na yaki da jahilci."

Yanzu haka dai a jamhuriyat ta Nijar mata ne suka yi yawa a makarantun yaki da jahilci, kasance tun suna yara ba a sa su makaranta ba.