1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin farfado da harkokin ciniki a taron APEC a Hanoi

November 18, 2006
https://p.dw.com/p/BubK

Shugabannin kasashen yankin Asia da fasifik sun bayyana cewa ,ashirye suke wajen kara rage kudaden haraji kayayyakin amfanin gona,domin sake farfado da tattaunawar inganta harkokin ciniki a duniya,baya ga rikicin nuclearn koriya ta arewa daya mamaye zauren taron nasu da aka bude yau a birnin Hanoi.A sanarwar farko da aka gabatar a dangane da wannan taro na yini biyu ,shugabannin kasashen dake kungiyar ciniki da tattali na Asia da Facifik din,sunyi alkawarin cimma wannan buri nasu ,domin farfado da harkokin tattalin arziki da kasuwanci.Kungfiyasr ta APEC dai itace ke wakiltar rabin fannin ciniki da kasuwanci na duniya.Kasar Malasia a taron dai,ta koka dangane da harkokin tsaro musamman tun bayan harin 11 ga watan satunba akan Amurka.Premiern Malasia Abdullah Badawi,ya jaddada bukatar daukan matakai a bangaren kasashen kungiyar.