1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin gano mafita a rikicin makiyaya da manoma

January 17, 2018

Bayan ganawa a tsakanin shugaban Najeriya da shugabannin al’ummar Benue kan rikicin makiyaya da manoma, an zargi bangaren gwamnati da sakaci.

https://p.dw.com/p/2r2LV
Nigeria Konflikt Farmer Pastoralisten
Hoto: DW/K. Gänsler

Duk da cewar dai ganawar da ke tsakanin mahukuntan na Abuja da jagororin al'ummar Benue ta kai bude sabon fata a kokari na kaiwa ya zuwa karshen rikicin, daga dukkan alamu kuma tana shirin bude sabon miki cikin kasar inda yanzu haka fadar gwamnatin kasar ke shan sukar nunin fifiko.

Dattawan Benue din ne dai suka nemi tozali da shugaban kasar da nufin koke dama fadin ra'ayinsu game da kokari na zama na lafiya a halin yanzu.

To sai dai kuma sassa dabam-dabam cikin kasar na kallon da walakin ware dattawan Benue ba tare da tozali da 'yan uwansu Fulanin ba da nufin ji daga daukaci na bangarorin domin yanke hukunci a bangare na gwamnati.

Siyasa ta shiga cikin batun

Shugabannin kungiyar Miyyetti Allah Cattle Breeders ta Fulanin dai sun ce ba su nemi suga shugaban kasar ba sannan kuma ba'a aika da goro na gaiyyata a garesu domin hada tozali da yan uwansu na Benue a cikin fadar ba a fadar Muhammad Ardo Kirua da ke zaman shugaba na kungiyar da kuma ya ce da sauran tafiya kafin iya kaiwa ga kama hanyar gyara.

"Akwai dalilin da ya sa suka je suka ga shugaban kasa. Mun sha fada wa mutane cewa akwai wasu abubuwa a boye. Ana amfani da maganar Fulani kan maganar siyasa. Shi ya sa maganar siyasarsu ta Benue ta kai su. Mun hadu da su a Benue da Nassarawa, da kamata ya yi a je Nassarawa ko a zo Abuja mu hadu mu da su. Zuwa wajen shugaban kasa su kadai ba shi ne zai warware matsakar ba."

Ana zargin gwamnatin Buhari da yi wa rikicin makiyaya da manoma rikon sakainar kashi
Ana zargin gwamnatin Buhari da yi wa rikicin makiyaya da manoma rikon sakainar kashiHoto: picture alliance/AP Photo/S. Aghaeze

Siyasa a cikin rikici ko kuma kokarin neman mafita dai, a fadar kakakin fadar gwamnatin kasar mallam Garba Shehu, gwamnatin kasar na kallon rikicin ne da idanu na basira maimakon idanu na siyasar da ke neman makantar da wasu ya zuwa yanzu.

Gwamnati ta dukufa don warware rikicin

"Shugaba Muhammadu Buhari bai son ya sa siyasa cikin wannan rikicin, domin da yana son ya sa siyasa ai da ya tashi ya je Benue. Harka ce ta damu kasa a fannin tsaro da yake so a yi maganinta tukuna sannan a ga abin da zai biyo baya. Kofar fadar shugaban kasa a bude take ga kowa."

Duk da cewar dai ana kallon rikicin na da ruwa da tsaki da gwagwarmayar neman na tuwo, ga Ardo Kirua, rikicin ya fi kama da siyasa maimakon kokari na shafun kashin kaji a rigunan na Fulani.

"Yanzu in ka ce rikicin manoma da makiyaya ne ake yi a Najeriya, to su jiraran da aka kashe 'yan wata uku uku da matan da aka kashe, su manoma ne ko makiyaya? In ka ce rikici ne an ce za a yi doka ta hana kiwo a fili, Mambila sun yi shekara fiye da 140 suna ware filin kiwo kamar yadda aka ce a yi, amma an je an kashe su."

Mahukunta dai sun ce suna kokarin neman mafitar rikicin da ke sauyin salo da launi da kuma ke iya rikidewa ya zuwa gwagwarmaya ta siyasa ta kasar a gaba.