1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dole sai Najeriya ta dage za ta kawar da Polio

Uwais Abubakar Idris
June 19, 2018

Hukumar tantance kasashen Afrika daga cutar shan inna ta bayyana cewa Najeriya sai ta kara dagewa kafin kaiwa ga matakin samun amincewar ta kawar da cutar ta Polio tsakanin al'umma.

https://p.dw.com/p/2zqCR
Nigeria Polio Virus
Hoto: Getty Images/AFP/P. Utomi Ekpei

Kokari na jajircewa game da kawar da cutar shan inna tun bayan da Najeriya ta samu koma baya a shekarar 2016 inda a garin Mongunu na jihar Borno aka sake samu bullar cutar a wancan lokaci dai dai lokacin da kasar ta yi nisa da kaiwa ga samun kawar da ita, wannan ya sanya a yanzu hukumar lafiya  dubawa a tsanake halin da Najeriyar ke ciki.

Kama daga hobasa na gudanar da allurer rigakafin da ma dakile buga alkaluma na boge na yara kanana da aka yiwa rigakafi ya sanya Najeriyar kawai ga wannan matsayi, inda  tun 2016 rabon da a samu bullar cutar, to sai dai duk da wannan ci gaba me ka jan kasar baya ne? Farfesa Rose Gana Leke it ace sakatariyar hukumar baiwa kasashen Afrika shaidar kawar da cutar shan inna ta Majalisar dinkin duniya.

Ta ce a dauki lokaci nahiyar Afrika na mamaki shin me ke faruwa ne da batun yaki da cutar shan inna a Najeriya, amma a gaskiya an samu ci gaba sosai kuma mun yi8 farin ciki da wannan,amma kasan abinda ya faru a baya mun kai watani sama da 20 sai kawai muka sake samun bullar cutar a wadanacan wurare da ba'a iya shiga, to a yanzu ma bamu san me ke faruwa a yankunan da ake yakin Boko Haram ba, wannan it ace matsalar, har yanzu akwai sauran wuraren da bamu san ko akwai cutar shan inna ba ko babu''

Baya daga matsala da sassan da ake fama da rashin tsaro Najeriyar ma ta fuskanci batu na zarge coge a kan alkamuman da aka samarwa a game da adadin allurara rigakafin da aka yi. Ko mahukuntan Najeriya sun gamsu da matakin da ake a yanzu? Dr Usman Saidu Adamau babban jami'in daukin gaggawa a harakar cutar shan inna a Najeriyar.

Tun da farko dai said a wakilin kungiyar lafiya ta duniya da ke Najeriya Dr Wondi Alemu ya bayyana bukatar kara kaimin da Najeriya ke yi a yaki da cutar shan inna da ma sauran kasashen Afrika da ke fama da matsalar domin akwai bukatar aiki tukuru.