1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen rikicin manoma da makiyaya

November 24, 2016

An yi taro domin neman hanyoyin kawo karshen rikici tsakanin manoma da makiyaya cikin kasashen Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/2TCDJ
Somalia Äthiopien Viehzucht-Nomaden
Hoto: DW/J. Jeffrey

A wani mataki na magance rigingimu tsakanin manoma da makiyaya na tsakanin kasa da kasa, kungiyoyin makiyaya daga Tarayyar Najeriya da suka hada da Miyetti Allah da kuma FNEN DADDO daga Jamhuriyar Nijar da sauran kananan kungiyoyin makiyaya da manoma daga kasashen guda biyu suka gudanar da taron domin lalubo hanyoyin da ke hadasa rigingimu tsakanin manoma da kuma makiyaya gami da irin wahalhalun da  makiyaya ke cin karo da su a tsakanin iyakokin kasashen guda biyu.

A young fulani herdsmen
Hoto: DW


Taron kasa da kasar ya hada kungiyoyin makiyaya da manoma a tsakanin kasashen biyu inda bayan mahawara mai zafi da canjin ra'ayoyi, wakilan taron suka tsaida cewar hanyoyin magance ringigimu na tsakanin manoma da makiyaya da kuma irin halin kuncin da makiyayan kasashen biyu ke fuskanta a bakin iyakoki  sai an hada karfi da karfe inji Alhaji Hassan Kuraye shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah daga Jahar Katsina da ya halarci taron.

A small farm of maize
Hoto: DW


Ba yau ba bangarorin manoma da makiyaya ke cin karo da matsala walau ta sace-sacen dabbobi daga bangaren makiyaya sai kuma ta barnar ganganci daga bangaren manoma  wani lokaci a kan samu asara ta rayuka.


Taron dai ya samu halartar jami'an tsaron gadun daji da alkalan kotuna daga kasashen biyu gami da sarakunan gargajiya  da duk wani mai fada aji a ci gaban tatalin noma da kuma kiwo tare da daukan matakan gudanar da taruruka lokaci zuwa lokaci a tsakanin kasashen biyu.