1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin kawo karshen rikicin Sudan ta Kudu

Yusuf BalaFebruary 26, 2016

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa dole ne masu gaba da juna a Sudan ta Kudu su tabbatar da gwamnatin hadin kan kasa dan rage mawuyacin hali da al’umma ke ciki.

https://p.dw.com/p/1I2s3
Ban Ki-moon in Südsudan
Ban Ki-Moon tare da Shugaba Salva KiirHoto: Reuters/J. Solomon

Ziyarar ta kwana daya da Ban Ki-Moon ya kai wannan kasa na zuwa ne bayan da ake ta samun jan kafa ga shirin kafa gwamnatin hadin kan kasa, abin da ke zama zagon kasa ga yarjejeniyar da aka cimma a watan Agusta na shekarar bara. Shi dai Riek Machar ya jaddada cewar ba zai sanya kafarsa a birnin Juba ba tare da dakarunsa 3000 da 'yan sanda ba, sannan a tura wasu dakarun 1200 a yankin kogin Nilu da yankunan Malakal da Bentiu da ke da arzikin mai. Ban Ki-Moon dai ya sake jaddada tsananin wahala da al’ummar wannan kasa ke ciki wadda ke bukatar sake kulawar shugabanin.

Ban Ki-moon in Südsudan
Ban Ki-Moon a Sudan ta KuduHoto: Reuters/J. Solomon

"Zaman lafiya shi ke kan gaba a mulkin siyasa ku bi duk abin da ya dace wajen ganin zaman lafiya ya dore a wannan kasa ta hanyar sanya hannu a yarjejeniyar da za ta fara aiki a yanzu."

Duba da halin 'yunwa da wahala da al’ummar kasar ta Sudan ta Kudu ke ciki ya sanya Majalisar Dinkin Duniyar bayyana makudan kudade da ake bukata don tallafa wa al’ummar wannan kasa. A cewar Mista Ban Ki-moon hali na kaka na kayi da al’ummar wannan kasa ke ciki na kara tabarbarewa abin da ke nuni da cewar ana bukatar sama da miliyan dubu na dalar Amirka dan tallafa wa mutane miliyan biyar a cikin wannan shekara kadai.

Ban Ki-moon
Ban Ki-MoonHoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com

"Ina bayyana cewar Majalisar Dinkin Duniya za ta ba da kudi dala miliyan dubu 21 daga asusunta na agajin gaggawa don haka ina kira ga al'ummar kasa da kasa da su kawo wa al'ummar kasar ta Sudan ta Kudu agaji.

Kasar ta Sudan ta Kudu ta fada yakin basasa shekaru biyu da suka gabata bayan shugaba Kiir da Riek Machar suka shiga rikicin siyasa da ya rikide da jefa kasar cikin kaka ni ka yi dubban jama#a suka rasu kimanin miliyan biyu suka kauracewa muhallansu.