1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnatin Yemen ta yi watsi da bukatun 'yan tawaye

Suleiman BabayoMay 18, 2016

Kasar Kuwait ta nemi bangarorin Yemen da ke yakar juna da su ci gaba da zama kan teburin sulhu karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya domin kawo karshen rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/1Iq3x
Kuwait Irak Friedensgespräche Jemen Ould Cheikh Ahmed
Hoto: Getty Images/AFP/Y.Al-Zayyat

Firaminista Ahmed bin Dagher na kasar Yemen din dai ya yi watsi da batun kafa gwamnatin hadin gwaiwa da 'yan tawayen Houthi suka nema, a yayin tattaunawar neman kawo zaman lafiya a kasar. Tun farko Sarkin Kuwait Sheikh Sabah al-Ahmad al-Sabah ya bukaci bangarorin kasar Yemen din da ke rikici da juna kan su ci gaba da zama a kan teburin tattaunawar domin tabbatar da zaman lafiya, bayan wakilan gwamnati sun yi barazanar ficewa daga zaman sulhun da ke gudana karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya.

Sarkin wanda kasarsa ke daukar nauyin taron ya nemi ganin bangarori sun cimma matsaya. Tun farko ministan harkokin wajen kasar ta Yemen Abdulmalek al-Mikhlafi wanda ke jagorantar wakilan gwamnati wadda ke samun goyon bayan saudiya a wajen tattaunawar sulhun, ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda zaman tattaunawar ke tafiya da 'yan tawayen Houthi masu samun goyon bayan Iran.

Wani kiyasin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna fiye da mutane 6,400 ne suka hallaka, yayin da wasu kusan milyan uku suka tsere daga gidajensu sakamakon rikicin kasar ta Yemen.