1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin magance rikicin kasar Siriya

Salissou BoukariDecember 15, 2015

A wannan Talata ce a sakataran harkokin wajan Amirka John Kerry, zai gana da takwaransa na Rasha da kuma shugaban na Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow.

https://p.dw.com/p/1HNNf
Hoto: AFP/Getty Images

Hakan na zuwa ne kafin wani zaman taro da zai gudana kan kasar ta Siriya nan gaba a birnin New York na Amirka. Kasar ta Amirka dai na dogoro ne da Rasha wajan ganin ta shawo kan shugaban kasar Siriya Bashar Al-Assad, domin hawa kan teburin tattaunawa da 'yan tawayan kasar. Don kawo karshen yakin da ke addabar Siriyan tun daga shekara ta 2011, wanda kawo yanzu ya yi sanadiyyar rasuwar mutane fiye da dubu 250, da kuma wasu miliyoyin mutane da suka bar gidajansu.

Kasashen biyu dai na Rasha da Amirka, za su samu daidaito kan ranar gudanar da taron na birnin New York wanda ake sa ran zai gudana a ranar Jumma'a mai zuwa 18 ga watan Disamba.