1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin maido da shirin tsagaita wuta a Siriya

Mohammad Nasiru AwalMay 17, 2016

Kasashen da ke tuntubar juna kan rikicin Siriya na tattaunawa a birnin Vienna kan ceto yarjejeniyar tsagaita wuta tare kuma da farfado da tattaunawar zaman lafiya.

https://p.dw.com/p/1IpEA
Österreich Wien Syrien Friedensgespräche
Hoto: Reuters/L. Foeger

Wakilan kasashe da ke tuntubar juna kan rikicin Siriya sun hallara a birnin Vienna na kasar Ostriya inda a karkashin jagorancin sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov za su tattauna don ceto shirin tsagaita wuta da sake farfado da tattaunawar sulhun birnin Geneva. Wakilai daga kasashe 17 ciki har da ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ke halartar taron. A lokacin da ya isa birnin Vienna Steinmeier cewa ya yi.

"Taron na yau na da nufin samar da yanayin aiki da shirin tsagaita wuta da aka amince da shi ba ma a birnin Aleppo kadai ba, har da kewayensa. Dole mu gano hanyar komawa kan wata maslaha a siyasance. Yanzu haka an dakatar da tattaunawar birnin Geneva, amma a yau za mu yi kokarin dawo da 'yan adawa kan teburin sulhu don shawo kansu su koma tattaunawa da gwamnatin Siriya a Geneva."