1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin sasanta Sunni da Shia a Iraqi

October 20, 2006
https://p.dw.com/p/BufB

Nan gaba a yau ne a birnin Makka ake sa ran shehunan malamai na Shia da Sunni daga Iraqi zasu rattaba hannu kann yarjejeniyar dakatar da zubda jini a kasar Iraqi.

Shehunan malaman sun hallara suyi kira da murya guda ga jamaar Iraqi su dakatar da kashe kashen juna da sukeyi.

Manyan shugabannin sunni da shia dai sun aike da sakonnin goyon baya ga wannan taro duk da cewa ba zasu halarci taron ba.

Sai dai kakakin kungiyar kasashen musulmi yace ba tare da halartar manyan shugabanin bagarorin biyu ba da kyar ne taron ya samu nasara da ake bukata.