1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin tsugunar da yan gudun hijira a Somali

November 2, 2007
https://p.dw.com/p/C159

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Mdd tace mutane dubu 88 ne suka rasa gidajen kwanan su, a makon daya gabata, a kasar Somalia. Hakan a cewar hukumar ya samo asaline, sakamakon yawaitar rikice rikice na yan tawaye.Rahotanni dai a yau din nan, sun tabbatar da rasuwar wasu mutane 7 a birnin Magadishu.Al´amarin ya faru ne bayan wani dauki ba dadi daya wanzu ne, a tsakanin sojin kasar da kuma dakarun Kotunan Islama ne. Ko da yake al´amarin ya lafa yanzu, to amma rahotanni sun shaidar da cewa wasu yankunan birnin na fuskantar harbe harben bindigogi. A yanzu haka dai hukumar ta Mdd na kokarin tsugunar da wadannan mutanen ne da suka rasa gidajen kwanan na su.