1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin tura Sojin MDD zuwa Dafur

May 23, 2006
https://p.dw.com/p/BuxC

Manyan jakadun Majalisar ɗinkin duniya na nan na ƙoƙarin shawo kan gwamnatin shugaba Omar Hassaan al-Bashir na Sudan domin amincewa da dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya a lardin Dafur. Duk da yarjejeniyar sulhun da aka cimma a wannan watan tsakanin Gwamnatin Sudan, da babbar ƙungiyar yan tawayen Dafur, har yanzu ana cigaba da yin arangama tsakanin yan tawayen da yan bangan gwamnati na ƙungiyar Janjaweed. Ƙasar Sudan wadda ke fuskantar matsin lamba daga gamaiyar ƙasa da ƙasa ta ƙi amincewa da tura dakarun kiyaye zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya, tana mai cewa tura sojojin zai haifar da yanayi ne irin na ƙasar Iraqi, inda masu tsauraran raáyin islama za su riƙa kai farmaki a kan dakarun sojin wanda kuma zai ƙara dagula shaánin tsaro a ƙasar. To amma tun bayan sanya hannu a kan yarejejeniyar sulhun da aka cimma, gwamnatin ta Sudan ta ɗan sasauto daga matsayin ta. A yau ne Jakadan majalisar ɗinkin duniya Lakhdar Brahimi tare da wani wakili na musamman Hadi Annabi za su isa ƙasar Sudan domin tattaunawa da shugaba Omar al-Bashir.