1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin warware rikicin nukiliyar kasar Iran

Ibrahim SaniFebruary 24, 2006

Jami´an diplomasiyya na kasashen Russia da Sin sun isa kasar Iran don fara tattaunawar kwanaki uku

https://p.dw.com/p/Bu1T
Hoto: AP

A cewar bayanai da suka iso mana wannan yunkuri daga kasashen biyu yazo ne a kokarin da suke na ganin cewa ba a gabatar da kasar ta Iran a gaban kwamitin sulhu na Mdd, domin ladaftar da ita ta hanyar sakala mata takunkumi.

Duk da wannan yunkuri da kasashen biyu keyi, wata majiya ta tabbatar da cewa kasar Russia na cike da shakkun anya kwalliya zata biya kudin sabulu a game da wannan tattaunawa.

Haka suma masu kalailaice harkoki na siyasa, ra´ayi suke dashi irin na kasar ta Russia, da cewa babu wata alamar dake nuni cewa kasar ta Iran zata sauko daga matakin data dauka na ci gaba da sarrafa sanadarin na Uranium.

A waje daya kuma, kafafen yada labaru sun rawaito shugaba Vladimir Putin na Russia na fadin cewa, yana da kyakkyawan fatan kasar sa zata samo bakin zaren warware wannan rikici cikin ruwan sanyi a nan gaba.

A dai yau alhamis, an jiwo ministan harkokin wajen na Iran , wato Manouchehr Mottaki, dake ziyara a Indonesia na fadin cewa kasar sa na duba yiwuwar yarda da shawarar da kasar Russia ta gabatar mata, to sai dai har yanzu tana bukatar cikakken bayani a game da haka, kafin daukar mataki na karshe.

Kasar dai ta Russia tace zata sarrafawa kasar ta Iran sanadarin na Uranium ne a cikin kasar ta, a maimakon ita Iran ta ci gaba da hakan a cikin kasar ta ta.

Kasashen dai na Russia da kasar Sin dake cikin kwamitin sulhu na Mdd, nada kyakkyawar alaka, musanmamma ta bangaren makamashi da kasar ta Iran,wanda bisa hakan, ba zasu so a gabatar da kasar ta Iran a gaban kwamitin sulhun na Mdd ba.

Wannan dai rikici na batun nukiliyar kasar ta Iran yayi kamari ne, bayan da kasashen yamma suka zarge ta da kokarin kera makamin nukiliya a boye, da sunan na inganta hasken wutar lantarki ne.

Ba sau da ba sau biyu ba mahukuntan na Iran sun karya ta wannan zargi da cewa bashi da tushe balle makama, domin nukiliyar su ta habaka rayuwar yan kasar ce baki daya, amma bata tashin hankali ba.

A kuwa yayin da ake cikin wannan hali, kasashen na yamma na tunanin cewa kasar ta Iran na daukar matakai ne na tafiyar hawainiya a tattaunwar da suke da kasar Russia, don jinkirta daukar mataki na ladaftarwa daga bangaren Mdd.

A dai ranar 6 ga watan maris ne na wannan shekara ake sa ran hukumar kula da makamashin nukiliyar ta duniya, zata gudanar da taron kolin ta a birnin Vienna,wanda a lokacin ne zata kai karar kasar ta Iran a gaban kwamitin sulhu na Mdd a hukuman ce, don duba yiwuwar lafardar da ita.