1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koma baya a ayyukan Amurka na yaki da taaddanci

Zainab A MohammedJune 17, 2005

Amurka na cigaba da fuskantar rashin goyon baya dacigaba da kasancewar dakarunta a cikin Iraki

https://p.dw.com/p/BvbH
Hoto: ap

Rahotanni nacigaba da nuni dacewa shugaba George W Bush nada magoya baya kalilan ne,ayanzu haka cikin ayyukansa na yakan taaddanci.Ko me ya haifar da wannan koma baya ta bangaren shugaban na Amurka?

Shekaru uku da rabi kenan da afkawa Amurka harin kunar bakin wake,wanda ya auku ranar 11 ga watan satumban shekarata 2001,amma sai gashi kokarin shugaba Bush na yaki da ayyukan taaddanci na cigaba da fuskantar adawa da kuma rashin goyon baya.

Wannan dai bazai kasa nasaba da irin matakan da Amurka ta dauka dangane da wannan batu da dokoki data kirkiro ba,da kurkunta dake Guantanamo Bay akasar Cuba,a hannu guda kuma da afkawa Iraki da karfin soji da Amurkan tayi babu gaira babu dalili.

Yanzu haka dai ana iya cewa Amurka na fuskantar matsaloli masu yawa dangane da yadda ta jagoranci mamayar Iraki,da kuma sakamakon abubuwanda suka ingizata fara yaki da ayyukan taadanci,inji masani kan harkokin siyasar rayuwa dake jamiar New York,Paul Light.

Wannan ya tunatar da bayanin wani dan majalisar Dottijai na jammiyar Republican Lindsey Graham ranar laraba,inda ya gabatar da wata sanarwa dake nuni dacewa, idan ba matakai aka dauka ba Amurka zata kwashi kashinta a hannu dangane da wannan yaki data sanya gaba.

Itama majalisar wakilai da akasanta da marawa gwamnati baya,ranar laraba tayi adawa da yanci da madafan iko da aka bawa hukumar bincike ta FBI ,tun bayan harin ranar 11 ga watan satumba 2001.

Ranar alhamis nedai yan majalisar wakilai Dennis Kucinich da Walter jones daga jammiyar Republican suka kaddamar da wani hadin gwiwa na daukan nauyin gabatar da shirin doka ,wanda ke marawa bukatar tsayar da lokacin janye dakarun Amurka daga Iraki.

Dan majalisa Jones yana mai raayin cewa an gano gaskiyar cewa babu makaman kare dangi balle dalilinsa,kuma ko iraki zata iya kera makaman nuclear ko bazata iya ba ,wannan ma an tabbatar da akasin haka,domin haka yakin da Amurka tayiwa jagoranci a wannan kasa da kuma cigaba da kasancewan dakarun kasar basu da wani tasiri.

Shugaba Bush dai yaki ya gabatar da lokaci da dakarun kasar zasu fara janyewa daga Iraki,batu daya raba kawunan yan majalisar kasar,wanda kuma ya jawo tofa albarkacin bakin Amurkawa.

Wani bincike na jin raayin jamaa da aka gudanar a wannan makon na nuni dacewa,kimanin sama da kashi 46 daga cikin 100 na wadanda aka ji raayinsu,ke bukatar a janye dakarun Amuraka daga Iraki.

Kazalika Kurkukun Guantanamo da Amurkan ke amfani dashi wajen tsare wadanda take zargi da ayyukan taaddanci na cigaba da samun suka daga alummomin duniya dama yan majalisar Amurkan,musamman tun bayan da kungiyar kare hakkin biladama taAmnesty ta bayyana yanayin muni da mugunta da ake aiwatarwa wadanda ke tsaren.

A dangane da hakane shugaban komitin yan majalisar Dottijai dake kula da sharia Arlen Specter ya bada shawaran cewa ,yan majalisar zasu gudanar da bincike,da kuma dokokin kula da wadanda ake tsare dasu a kurkukun,wadanda akalla yawansu yakai 500 ayanzu haka, kuma ake zarginsu da aikata ayyukan taaddanci,kana har yanzu baa gurfanar dasu gaban kowace hukumar bincike ba ,kuma basu da ikon isa kotunan hukunci,tunda aka tsare su.

Bayan lokaci mai tsawo ana kokawa da ayyukan yan tadda,yanzu a zaune take kashi 12 daga cikin 100 kachal na Amurkawa ne ke tsoron ayyukan taaddanci da kuma irin barazanar dazai iya haifarwa.Ayayinda kashi 58 daga Cikin 100 na Amurkawa na masu raayin cewa yakin Iraki da Amurkan ta jagoranta bai haifar musu da komai face halin ni yasu.